Home Back

Hukumar Kwallon Kafar Najeriya Ta Nada Sabon Kocin Tawagar Super Eagles

legit.ng 2024/5/18
  • Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta nada tsohon dan wasan Super Eagles Finidi George a matsayin sabon kocin kungiyar
  • An ruwaito cewa Finidi George, ya shafe watanni 20 a matsayin mataimaki ga tsohon kocin Super Eagles, José Santos Peseiro
  • Babban aikin sabon kocin shi ne jagorantar tawagar Najeriya zuwa ga nasarar shiga gasar cin kofin duniya na FIFA 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rahotannin da muka samu yanzu na nuni da cewa an nada Finidi George a matsayin sabon kocin tawagar Najeriya ta Super Eagles.

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta sanar da nadin Finidi a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Hukumar kwallon kafar Najeriya ta nada sabon kocin tawagar Super Eagles
Hukumar NFF ta nada Finidi George a matsayin sabon mai horar da tawagar Super Eagles. Hoto: @thenff Asali: Twitter

Finidi ya rike kocin rikon kwarya

Finidi George, wanda ya shafe watanni 20 a matsayin mataimaki ga José Santos Peseiro mai barin gado, ya kasance kocin rikon kwarya bayan tafiyar dan kasar Portugal din.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Punch ta rahoto cewa cikin wa'adinsa na wucin gadi, George ya jagoranci wasanni biyu na sada zumunta a Morocco a watan da ya gabata.

Tawagar ta kawo karshen rashin nasara na tsawon shekaru 18 tsakaninta da Ghana inda wasan ya tashi da ci 2-1, amma George ya sha kashi a hannun Mali da ci 0-2.

Nasarorin da Finidi ya samu a taka leda

Fitaccen dan wasan ƙwallon ƙafa, George, ya samu tarin lambobin yabo da suka hada da lambobin zinare, azurfa da tagulla daga gasar 1992, 1994, 2000 da 2002 AFCON.

Daya daga cikin abubuwan tunawa da George shi ne taimakawa marigayi Rashidi Yekini wajen zira kwallon farko ta Najeriya a gasar cin kofin duniya ta FIFA a karawarta da Bulgaria a Dallas, Amurka a ranar 19 ga Yuni 1994.

Aikin da ke gaban sabon kocin

Babban aikin sabon kocin shi ne jagorantar kungiyar zuwa ga nasara a wasanni biyu masu muhimmanci na neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya na FIFA 2026.

Najeriya za ta kara tsakaninta da Afrika ta Kudu da Jamhuriyar Benin a Uyo da Abidjan, cikin makonni biyar masu zuwa, rahoton jaridar Leadership.

Asali: Legit.ng

People are also reading