Manchester United da Liverpool za su sabunta hamayyar dake tsakanin su
INGILA – Yau ake saran kungiyar Manchester United ta kara da babbar abokiyar hamayyarta a shekarun baya, wato kungiyar Liverpool wadda ke hankoron lashe gasar Firimiya ta Ingila a wannan shekarar.
Wallafawa ranar: 07/04/2024 - 14:53
Minti 1
Wannan karawar ta yau na da matukar tasiri ga kungiyoyin guda biyu saboda muhimmancin wasan da kuma bukatar samun nasara domin ganin sun kara yawan makin da suke da shi a teburin Firimiyar.
Kungiyar Liverpool wadda yanzu haka ke matsayi na 2 da maki 70 a teburin gasar, na matukar bukatar wannan wasa domin kwace matsayin farko daga kungiyar Arsenal mai maki 71 sakamakon nasarar da kungiyar ta samu a kan Brighton da ci 3-0 a karawar jiya.
Ita kuwa Manchester United wadda ke matsayi na 6 da maki 48, na matukar bukatar maki 3 dake cikin wannan karawar a kokarin da take yi na ganin ta samu kare kakar bana a cikin wadanda za su samu damar zuwa gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a shekara mai zuwa.
A karawar da kungiyar ta yi da Chelsea a ranar alhamis da ta gabata, Manchester ta barar da damar da ta samu, abinda ya bai wa Chelsea damar doke ta da ci 4-3.
Masu sharhi a kan wasannin kwallon kafa na bayyana cewar, raunin da Chelsea ta yiwa kungiyar zai sa 'yan wasan ta su dage wajen ganin sun fidda kitse a wuta a karawar ta yau.
Samun nasarar Manchester zai taimakawa Arsenal damar ci gaba da zama na farko a teburin Firimiyar wadda kungiyoyi 3 da suka hada da Liverpool da Manchester City da kuma Arsenal ke fafatawa a kai.