Home Back

HAJJ 2024: Nasarorin da muka samu a Jihar Kaduna na da nasaba da kwarin gwiwar da gwamna Uba Sani ya bama – Amirul Hajji, Sarkin Lere

premiumtimesng.com 2 days ago
HAJJ 2024: Nasarorin da muka samu a Jihar Kaduna na da nasaba da kwarin gwiwar da gwamna Uba Sani ya bama – Amirul Hajji, Sarkin Lere

Sarkin Lere, na jihar Kaduna, Suleiman Umaru, ya yaba da goyon bayan da gwamnan Kaduna, Uba Sani ya ba hukumar Akhazai ta jihar da kuma musamman aikin Haji na bana.

Sarki Umaru, wanda shine Amirul Hajji na bana ya bayyana haka da ya ke hira da manema labarai a garin Maka ranar Laraba.

Sarkin ya kara da cewa an samu dimbin cigaba a yadda aka gudanar da aikin Haji a bana daga jihar inda ya jingina nasarorin da irin gudunmawar da gwamnan Sani na jihar ya baiwa hukumar.

” A Hajjin bana mun samu nasarori da dama wanda basu misaltuwa. Alhazan Kaduna ba su rasa komai ba. Soma daga wuraren kwana a Madina da abincinsu, zuwa Makka da kuma kiwon lafiyarsu.

” Saboda inganci tsare-tsarenmu har hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta umarci jihohi su yi koyi da irin yadda muka gudanar da namu shirin, da kuma yadda muke komai na mu cikin sauki da natsuwa.

Bayan haka ya jinjina kokarin jihar da a bana ta buɗe asibiti na ta na kanta a Makka, da ya sa Alhazai suka rika samun saukin neman magani ba tare da sun yi nesan kiwo zuwa waɗanda NAHCON ta buɗe ba.

” Idan Alhaji bashi da lafiya, sai ya garzaya asibitin mu a duba shi ya ƙarɓi magani. Dalilin haka ya sa cikin ikon Allah Alhazai biyu ne kacal Allah ya yi musu cikawa daga Kaduna a bana.

Bayan haka sai sarki Umaru ya godewa shugaban hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna Farfesa Salihu Abubakar bisa jagorantar kwararrun ma’aikata da ya yi a aikin na bana wanda hakan ne ya taimaka wajen samun nasararorin da aka samu a bana

Daga nan ya kuma yi alkawarin tabbatar da an mayar da Alhazai gida lafiya kuma a cikin tsari.

Ya ce ” Za a yi amfani da tsarin nan ne na wadanda suka fara shigowa sune za su fara komawa gida, kuma tuni aka fara raba jakkuna da shirye-shiryen fara tashi a cikin makon da za a shiga.

People are also reading