Home Back

Yaki da ci da gumin yara a Côte d’Ivoire

dw.com 2024/7/3
Côte d'Ivoire | Yaki | Kananan Yara | Noma | Coco
Yaki da amfani da kananan yara wajen noman coco Côte d'Ivoire

Idan ana batun alawar cakulan da dama kan yaba samfurinta a slab ko Tablette, ko ma sauran ragowar kayan tande-tande da makulashe da a kan yi wa lakabi da cakes da desserts. Ba wani biki da ke wucewa, ba tare da an yi amfani da alwara cakulan ba. Kiyasi ya nuna karfin jarin kamfanonin sarrafa cakulan a duniya ya kai kusan dalar Amurka biliyan 140. To amma duk da haka akwai wani abu da ya kamata a sani game da wannan daraja ta cakul an, wato ci da gumin kananan yara. Fiye da kaso 60 cikin 100 na Cocon da kamfanoni ke amfani da shi, na fitowa ne daga kasashen Ghana da Côte d'Ivoire. Manoman wadannan kasashen ba sa samun wata riba da ka iya ba su damar daukar ma'aikata majiya karfi, suna amfani da yara ne kanana ko 'ya'yansu ko kuma 'ya'yan dangi. Wannan ya sa manoman Coco ke taimakawa gaya, wajen amfani da yara a aikin karfi ko kuma ci da guminsu a nahiyar Afirka. Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO), ta kiyasta cewa yara sama da miliyan 86 ne ke cikin wannan tarkon.

Sai dai kuma kasar Côte d'Ivoire na kokarin ganin ta fita daga wannan kangin ta hanyar kafa kwararan matakai na kare kananan yaran daga amfani da su wajen aikin noman Coco a masana'antun, kuma tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu. Wasu daga cikin hanyoyin da gwamntin kasar ta bijiro da su, sun hadar da tilasta wa kowane yaro zuwa makarantar boko da kuma bayar da ilimi kyauta a makarantun. Bugu da kari kasashe masu dimbin arzikin Coco kamar Ghana da Côte d'Ivoire, sun himmatu a kan hanyoyin habaka darajar Coco tare da tallafi mai gwabi ga manomansa domin cike musu gibi. A ka'idance ya kamata a ce wadannan dabarun, sun taka muhimmiyar rawa a masana'antun Coco. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba a kasa kamar Côte d'Ivoire manoman Coco na rayuwa ne a karkara, saboda haka yana da matukar wuya hukumomi su bi shirin sau da kafa. Sannan kuma wata babbar matsala ita ce matsin tattalin arziki da ke addabar yammacin Afirka, na barazana ga wadannan matakai ma su matukar muhimmanci da suka taimaka wa kasar ta kama hanyar yin bankwana da wannan matsala ta ci da gumin kananan yara. Duk da haka, Côte d'Ivoire ta samu ci-gaba a yakin da take da ci da gumin kananan yaran da ke ba wa cakulan wani dandano mai tsami da ke biyowa baya.

People are also reading