Home Back

Yajin Aiki: Ma'aikatan Gwamnati a Jihar Kano Sun Bi Umarnin Kungiyoyin NLC da TUC

legit.ng 2024/7/6
  • Ma'aikatan gwamnati a Kano sun yi zamansu a gida yayin da NLC ta ayyana shiga yajin aiki daga yau Litinin, 3 ga watan Yuni
  • An kulle sakateriyar Audu Baƙo yayin da aka tsayar da duk wasu harkokin sufuri a filin sauka da tashin jiragen sama na Aminu Bando ban da jirgin alhazai
  • Sai dai ƴan kwasuwa a manyan kasuwannin Kano sun fita sun ci gaba da harkokin su yayin da bankuna kuma duk a garƙame su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Ma'aikatan gwamnati a jihar Kano sun bi sahun takwarorinsu, sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani yau Litinin, 3 ga watan Yuni, 2024.

Wanna na zuwa ne bayan manyan kungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da TUC sun sanar da shiga yajin aiƙi kan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Shugaban NLC, Joe Ajaero.
Ma'aikata sun bi sahun ƴan uwansu, sun shiga yajin aiki a Kano Hoto: Nigeria Labour Congress Asali: Facebook

Wakilin jaridar Leadership ya tattaro cewa sakateriyar gwamnatin tarayya da ta jiha da ke Audo Bako an kulle su da kwaɗuna, babu ma'aikacin da ya fito aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wuraren aiki waɗanda aka saba gani cike da jama'a har da cunkoso sun zama babu kowa yau Litinin saboda ma'aikata ba su fito aiki ba.

Amma a ɓangaren ƴan kasuwa kuwa, babu abin da ya sauya, mutane sun ci gaba da harkokin su na kasuwanci a jihar Kano.

Kasuwar IBB, kasuwar Kantin Kwari, Kasuwar Rimi da kasuwar hada-hadar wayoyi Farm Centre ba ma su san ana yajin aiki ba, mutane suna harkokin su na yau da kullum.

A filin jirgin sama na Aminu Kano kuma, jiragen da ke jigilar alhazai ne kawai aka bari suka tashi amma duk wani jirgin sama an dakatar da shi saboda yajin NLC.

Bugu da ƙari, dukkan bankunan da wakilim jaridar ya ziyarta a kwaryar birnin Kano ya tarar da su a kulle ba su aiki.

Ƴan kwadagu sun bayyana cewa wannan yajin aikin babu wasa a cikinsa saboda sun fahimci gwamnatin tarayya ba ta ɗauki batun mafi ƙarancin albashi da gaske ba.

Gwamnati ta kira taro da NLC

A wnai rahoton kuma kun ji cewa yayin da yajin aiki ƴan kwadago ke ƙara kankama, gwamnatin tarayya ta kira taron kwamitin mafi ƙarancin albashi.

Hukumar kula da albashi da kuɗin shiga ta ƙasa (NSIWC) ce ta kira taron wanda zai gudana ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024

Asali: Legit.ng

People are also reading