Home Back

DAGA KANO: Gwamna Abba ya umarci sarakunan da aka tsige su fice daga fadar su cikin sa’o’i 48

premiumtimesng.com 2024/9/28
KANO: Gwamna Abba ya ce zai sa hannu kan hukuncin da kotu za ta yanke wa wanda ya cinna wa masallata wuta har 17 suka rasu

Gwamna Abba Kabir-Yusif na Kano ya umarci sarakuna biyar da aka tuɓe su fice daga fadar su cikin sa’o’i 48.

Tsigaggun sarakunan dai sun haɗa da Aminu Ado na Birni da Kewaye, na Bichi Nasiru Ado, na Rano, Ƙaraye.

Haka kuma gwamnan ya umarce su kai wa Mataimakin Gwamna, Aminu Abdulsalam takardar ajiye aikin su.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Gwamna Abba Gida-gida ya maida Muhammadu Sanusi II Gidan Dabo.

Gwamnan Kano Abba Kabir-Yusif ya maida Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki.

Ya rattaba hannun amincewa, jim kaɗan bayan da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano da tawagar sa suka gabatar masa da sabuwar dokar Masarautar Kano, wadda ta rushe dokar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta yi.

Gwamna ya rattaba wa dokar hannu, dama kuma manyan hakimai masu naɗa sarki sun hallara a Gidan Gwamnatin Kano, bayan Kakakin Majalisa ya kai sabuwar doka.

Ba yau aka fara ƙirƙirar masarautu kuma aka rushe su ba. A 1981 tsohon Gwamnan Kano, Marigayi Abubakar Rimi ya ƙirƙiri masarautun Gaya, Auyo, Rano da Dutse. Da Sabo Bakin Zuwo ya zo ya ya hau mulki a 1983, rusa su, ya maida Kano yadda take.

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa An maida Sarki Muhammadu Sanusi lokacin da ya ke halartar taro a Jihar Ribas.

Majiya ta tabbatar da cewa Tuɓaɓɓen Sarki Aminu Ado ba ya Kano, ya na ziyara a wata jiha daga jihar Kudu maso Yamma, shi kuma Nasiru Ado na Bichi, an ce ba ya ƙasar.

People are also reading