Home Back

An Daure Malami shekaru 20 Kan Sukar Gwamnatin Saudiyya

leadership.ng 2024/8/21
An Daure Malami shekaru 20 Kan Sukar Gwamnatin Saudiyya

Saudiyya ta yanke wa wani malamin makaranta, Asaad al-Ghamdi mai shekaru 47 hukuncin daurin shekara 20 a gidan yari saboda sukar gwamnati a shafukan sada zumunta.

An kama shi a watan Nuwamban 2022 a birnin Jeddah, kuma aka yanke masa hukunci a ranar 29 ga Mayu a wata kotu ta musamman, inda aka zarge shi da ta’addanci.

Takardun kotu sun nuna cewa an tuhumi Ghamdi da “kalubalantar addini da adalcin Sarki da Yarima” da “wallafa jita-jita da labarun karya.”

Shaidun da aka gabatar sun haɗa da rubuce-rubucen da ya suka soki ayyukan ‘Vision 2030’ da nuna alhininsa ga mutuwar dan gwagwarmaya Abdallah al-Hamed.

Lamarin Ghamdi ya yi kama da na dan uwansa Mohammad, wanda aka yanke wa hukuncin kisa a bara saboda yada wasu rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta.

Dan uwansu na uku, Saeed, wanda malamin addini ne da ke gudun hijira, ya yi Allah-wadai da hukuncin, inda ya ce babu komai game da tuhume-tuhumen face zalunci.

A cikin ’yan shekarun nan, kotunan Saudiyya sun yanke hukuncin daurin shekaru masu tsawo ga mutane da dama saboda rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta, ciki har da Nourah al-Qahtani da aka yanke wa hukuncin shekara 45 da Salma al-Shehab da aka yanke wa hukuncin daurin shekara 34.

Akwai Manahel al-Otaibi, wadda aka yanke wa hukuncin shekara 11 saboda kalubalantar dokokin Saudiyya game da sanya sanya abaya ga mata.

People are also reading