Home Back

Yajin Aikin NLC: An Rufe Tushen Wutar Lantarki Na Najeriya, a Shirya Kwana a Duhu

legit.ng 2024/10/5
  • Kamfanin kula da rarraba wutar lantarki na Najeriya ya sanar da jama’a cewa kungiyar kwadago ta rufe tushen wutar lantarki na kasa
  • An ruwaito cewa an rufe ginin tushen wutar da misalin karfe 2:19 na safiyar ranar Litinin, abin da ya jawo daukewar wuta a fadin kasar
  • A ranar Litinin 3 ga watan Yuni ne kungiyar kwadago ta fara yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar kan sabon mafi karancin albashi

FCT, Abuja - Kamfanin kula da rarraba wutar lantarki na Najeriya ya sanar da jama’a cewa kungiyar kwadago ta rufe tushen wutar lantarki na kasa.

Kungiyar kwadago ta rufe tushen wutar a daidai lokacin da kungiyar kwadago ta NLC da TUC suka fara yajin aikin sai baba-ta-gani a fadin kasar.

TUC ta yi magana kan dauke wutar lantarki a Najeriya
Saboda yajin aikin kungiyoyin kwadago, an rufe tushen wutar lantarki na Najeriya. Asali: Getty Images

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito a safiyar ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, rufe tushen wutar ya haifar da daukewar wuta a fadin kasar.

An rufe ginin tushen wutar da misalin karfe 2:19 na safiyar ranar Litinin, abin da ya jawo daukewar wuta a fadin kasar kamar yadda rahoton jaridar Leadership ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yajin aiki: Sanarwar TUC

A wani bangare na sanarwar, TUC ta bayyana cewa:

“Da misalin karfe 1:15 na safiyar yau ne, jami'in kula da rarraba wuta na Benin a karkashin kungiyar TCN ya sanar da cewa an kori dukkanin ma’aikata daga wajen aikin.
"An yi wa ma’aikatan da suka yi turjiya duka, in da wasu kuma suka samu raunuka a yayin da ake kokarin fitar da su daga dakin da ake kula da rarraba wutar, an bar wajen ba kowa."

TUC ta lissafa sauran kananun tashoshin rarraba wutar da kungiyar kwadago ta rufe sun hada da Ganmo, Benin, Ayede, Olorunsogo, Akangba da Osogbo.

Majalisar tarayya ta gana da 'yan kwadago

A jiya Lahadi, muka ruwaito cewa shugabannin majalisar tarayya sun gana da shugabannin kungiyar kwadago domin dakatar da ma'aikatan daga shiga yajin aiki.

Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da Festus Osifo na TUC ne suka wakilci 'yan kwadago yayin da Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas suka wakilci bangaren majalisar tarayyar.

Asali: Legit.ng

People are also reading