NDLEA ta Gargadi Matafiya Kan Hanyar da Ake Iya Aukawa Cikin Matsla
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Lagos-Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta gargadi matafiya da kada su kuskura su yi rikon jakar da ba su san abin da ke ciki ba.
NDLEA ta yi gargadin za a iya rikon jaka mai dauke da kwayoyi da sauran abubuwan maye da zai zama gagarumin laifi, musamman idan aka kama wanda ke dauke da jakar.
Daraktan yada labaran hukumar, Femi Babafemi ne ya yi gargadin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X yau Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana fargabar wadanda ba su ji ba su gani ka iya fuskantar hukunci idan aka kama su da jakunkunan masu dauke da kwayoyi da sauran kayan maye.
Femi Babafemi ya bayyana cewa hukumomi a wata kasa sun cafke wasu yan Najeriya guda biyu bayan an gano kwalaben kodin a jakar da wata daliba ta basu riko.
Dalibar, wacce ba a bayyana sunanta ba, ta bawa wasu dalibai biyu ciki har da mai karatun digiri na 3 sallahun jakarta.
Sai bayan hukumomi na duba jakunkunan matafiya kamar yadda aka saba sai aka gano kwalaben kodin din, kamar yadda kafar Channels Television ta wallafa.
A kalamansa:
" Da tuni suna gidan yari ba dan @ndlea_nigeria ta yi kokari wajen dawo da aihinin mai jakar gida ba "
"Wannan shi yasa mu ke jan kunne kada wanda ya dauki jakar da bai san abin da ke ciki ba daga hannun kowa."
A baya kun samu labarin yadda hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama wasu mutane 319 da ake zargi da ta'ammalli da miyagun kwayoyi a jihar Kano.
kwamandan hukumar reshen jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad ya shaidawa manema labarai cewa akwai mata 14.
Asali: Legit.ng