Ana Cikin Matsalar Rashin Tsaro, Shettima Ya Fadi Shirin Tinubu Kan 'Yan Bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi magana kan shirin Shugaba Tinubu na kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.
Kashim Shettima ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya ƙudiri aniyar magance ɗumbin kalubalen tsaro da ƙasar nan ke fuskanta.
Kashim Shettima ya bayyana haka ne a Kano a lokacin da ya karɓi baƙuncin wata tawaga ta shugaban ƙasa domin ta’aziyyar rasuwar surukarsa, Hajiya Maryam Albishir.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Stanley Nkwocha ya sanya a shafinsa na X a ranar Laraba.
Da yake yabawa ziyarar, mataimakin shugaban ƙasan ya sake nanata abin da ya bayyana a matsayin jagoranci na gaskiya na Tinubu, yana mai cewa shugaban ƙasan na nufin ƙasar nan da alheri.
"Komai nisan dare, gari zai waye. Tabbas muna fuskantar ƙalubalen tsaro a faɗin ƙasar nan, amma shugaban ƙasa a shirye yake wajen sauya ma'anar mulki na zamani, da jajircewa wajen magance matsalar rashin tsaron da ke addabar ƙasar nan."
"Ina so na yi kira a garemu da mu mara masa baya kan wannan ƙudirin na sa domin mu ceto ƙasar nan a tare. Ba batun ɗora alhaki kan wasu ba ne. Batu ne na tabbatar da cewa ƙasar nan ta yi aiki, sannan idan Najeriya ta yi aiki, Afirika za ta yi aiki."
- Kashim Shettima
Shettima ya nuna matuƙar godiyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Kano bisa karɓar baƙuncinsa da iyalansa na tsawon kwanaki uku.
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto kan yunƙurin da ta ke yi na cire Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar daga muƙaminsa.
Mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa mai alfarma Sarkin Musulmin ba wai kawai Sarki ba ne a Sokoto, darajarsa da ƙimarsa sun wuce hakan.
Asali: Legit.ng