Home Back

Kano: Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Rikakkun 'Yan Damfara, an Kwato Kayan Aiki

legit.ng 2024/7/1
  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu ƴan damfara da suka ƙware wajen yin alat na bogi
  • Ƴan damfaran an cafke su bayan sun damfari wani gidan mai maƙudan kuɗaɗen da suka kai N300,000 yayin da suka siya man dizal
  • Waɗanda ake zargin bayan sun amsa laifinsu, an kuma ƙwato injinan POS guda 22 da katunan cirar kuɗi na ATM guda 52 a hannunsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Ƴan sanda a Kano sun kama wasu da ake zargin ƴan damfara ne waɗanda suka ƙware wajen samar da alat ɗin banki na bogi.

Rundunar ƴan sandan jihar ta ce an ƙwato injinan POS guda 22, katunan ATM guda 52, jarkokin man dizal guda takwas, da wayoyin hannu guda shida.

'Yan sanda sun cafke 'yan damfara a Kano
Dubun wasu 'yan damfara ta cika a Kano Hoto: Kano Police Command Asali: Twitter

Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin rundunar na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun cafke ƴan damfara a Kano

Abdullahi Kiyawa ya ce bayan samun rahoton, kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, ya umarci jami’an tsaro da su kasance cikin shiri domin tabbatar da kama waɗanda suka aikata laifin tare da hukunta su.

"A ranar 05/06/2024 da misalin ƙarfe 8:45, jami’an ƴan sanda sun samu kiran gaggawa daga manajan gidan mai na Chula."
"Bayan sun garzaya gidan man sun kama Abdulkadir Ibrahim mai shekaru 38 na unguwar Naibawa da Aliyu Tukur mai shekaru 27 na unguwar Kuntau a Kano."
"Waɗanda ake zargin sun sayi man dizal na N300,000 a gidan mai na Chula ta hanyar amfani da hanyoyin biyan kuɗi na bogi wanda hakan ya sanya masu gidan man suka samu alat na bogi."

- Abdullahi Haruna Kiyawa

Shin ko sun amsa laifinsu?

Ya bayyana cewa a lokacin bincike, waɗanda ake zargin sun jagoranci ƴan sanda domin cafke Auwal Ibrahim mai shekaru 20 na unguwar Na'ibawa, wanda shi ne ya karɓi man dizal ɗin.

A cewar kakakin ƴan sandan, waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu tare da amsa cewa sun damfari masu ba da mai a gidajen mai na AY Maikifi, Aliko, da sauran wuraren kasuwanci a Kano.

Ƴan sanda na neman ƴan daba a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ta fara farautar wasu iyayen daba 13 da ake zargi da ƙoƙarin dawo da faɗan daba a wasu sassan jihar.

Rundunar ta aika da jami'anta zuwa unguwanni da ake fargabar sake ɓarkewar faɗan daban domin yin caraf da ɓata garin.

Asali: Legit.ng

People are also reading