Home Back

Yajin Aikin NLC: Majalisar Dattawa Ta Aika Bukata Ga Tinubu Kan Albashin Ma’aikata

legit.ng 2024/7/3
  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ci gaba da biyan kyautar karin albashi na N35,000
  • Godswill Akpabio ya mika wannan bukatar ga gwamnati a daren jiya Lahadi, 2 ga watan Mayu bayan tattaunawa da 'yan kwadago
  • Majalisar dattawa ta ce ta nemi ganawa da 'yan kwadagon ne domin duba yiwuwar hana su fara yajin aikin da suka fara yau Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ci gaba da biyan kyautar karin albashi na N35,000 ga ma'aikatran kasar.

Majalisar dattawa ta yi magana kan albashin ma'aikata
Majalisar dattawa ra nemi gwamnatin tarayya ta ci gaba da ba ma'aikata kyautar N35,000. Hoto: @NLCHeadquarters Asali: Twitter

Majalisar ta ba da wannan shawarar ne yayin ga kwamitin tattaunawa da ba gwamnati shawara kan mafi karancin albashi ya gaza kammala aikin sa.

An tattauna tsakanin majalisa da NLC

Jaridar Vanguard ta ruwaito shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya mika wannan bukatar ga gwamnatin tarayya a daren jiya Lahadi, 2 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jiya ne muka ruwaito cewa shugabannin majalisar dokokin tarayya da shugabannin kungiyoyin kwadago suka saka labule a babban birnin tarayya Abuja.

Godswill Akpabio ya ce sun nemi ganawa da 'yan kwadagon ne domin duba yiwuwar hana su fara yajin aikin da suka kuduri shiga a ranar Litinin, 3 ga watan Mayu (yau).

Akpabio ya roki NLC ta janye yajin aiki

Sai dai kamar yadda muka ruwaito, an tashi wannan taro ba tare da an samu wata nasara ba inda 'yan kwadagon suka ce ba za su iya dakatar da shiga yajin aikin ba.

Shugaban majalisar dattawan ya ce:

“Mun dade muna rokon NLC da TUC da su hakura da yajin aikin da ake shirin shiga, mu koma kan teburin tattaunawa domin warware matsalar.
"Ina roko da a dakatar da yajin aikin domin a ci gaba da tattaunawa ta yadda hakan zai zama mafi amfanin 'yan Najeriya da kuma kasa.r baki daya"

An rufe tushen wutar lantarki na kasa

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar kwadago ta rufe tushen wutar lantarki na kasa sakamakon fara yajin aikin da ta shiga yau Litinin.

Hukumar kula da rarraba wutar lantarki ta Najeriya ta bayyana hakan, inda ta yi nuni da cewa za a samu daukewar wutar lantarkin a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

People are also reading