Home Back

Kano: Fitaccen Basarake Ya Magantu Kan Dawo da Sanusi II, Ya Tura Masa Sako Na Musamman

legit.ng 2024/7/1
  • Sarki Muhammadu Sanusi II yana ci gaba karbar sakwannin taya murna daga manyan sarakuna da ƴan siyasa
  • Sarkin Gwandu a jihar Kebbi, Manjo-janar Muhammad Ilyasu Bashir shi ma ya taya Sarkin murnan dawowa kujerar sarautar Kano
  • Sarkin ya ce tabbas wannan nadin ya yi dai-dai duba da kwarewa da kuma jajircewa irin na Muhammadu Sanusi II

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kebbi - Sarkin Gwandu a jihar Kebbi, Manjo-janar Muhammad Ilyasu Bashir mai ya taya Sarki Muhammadu Sanusi II murna.

Ilyasu Bashir ya tura sakon murnan ne ga Sanusi II bayan dawowa kan kujerar sarautar Kano a kwanakin baya.

Sarkin Gwandu ya tura sako ga Sanusi II a Kano
Sarkin Gwandu, Muhammad Ilyasu Bashir ya taya Muhammadu Sanusi II murnan dawowa kujerar sarautar Kano. Hoto:@opeyemtech. Asali: Twitter

Sarkin Gwandu ya taya Sanusi a murna

Mai Martaba ya ce wannan ba karamin ci gaba ba ne duba da kwarewa na Sarki Sanusi II, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin ya kuma roki Allah ya ba Sanusi II hikima da kwazo wurin gudanar da shugabanci ba tare da nuna wariya ba.

Har ila yau, sarkin ya bukaci al'umma da su zauna lafiya da juna yayin da ake rigimar sarauta a jihar.

Ƴaƴan Dahiru Bauchi sun ziyarci Sanusi II

A wani labarin, kun ji cewa Ƴaƴan Sheikh Dahiru Bauchi sun kawo ziyara fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a jiya Litinin.

Tawagar karkashin jagorancin Aminu Dahiru Bauchi ta kai ziyarar domin nuna goyon baya ga Sarkin tare da nuna jin dadinsu.

Wannan na zuwa ne bayan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero tare da mayar da Muhammadu Sanusi II kujerar.

Asali: Legit.ng

People are also reading