Kano: Fitaccen Basarake Ya Magantu Kan Dawo da Sanusi II, Ya Tura Masa Sako Na Musamman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kebbi - Sarkin Gwandu a jihar Kebbi, Manjo-janar Muhammad Ilyasu Bashir mai ya taya Sarki Muhammadu Sanusi II murna.
Ilyasu Bashir ya tura sakon murnan ne ga Sanusi II bayan dawowa kan kujerar sarautar Kano a kwanakin baya.
Mai Martaba ya ce wannan ba karamin ci gaba ba ne duba da kwarewa na Sarki Sanusi II, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin ya kuma roki Allah ya ba Sanusi II hikima da kwazo wurin gudanar da shugabanci ba tare da nuna wariya ba.
Har ila yau, sarkin ya bukaci al'umma da su zauna lafiya da juna yayin da ake rigimar sarauta a jihar.
A wani labarin, kun ji cewa Ƴaƴan Sheikh Dahiru Bauchi sun kawo ziyara fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a jiya Litinin.
Tawagar karkashin jagorancin Aminu Dahiru Bauchi ta kai ziyarar domin nuna goyon baya ga Sarkin tare da nuna jin dadinsu.
Wannan na zuwa ne bayan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero tare da mayar da Muhammadu Sanusi II kujerar.
Asali: Legit.ng