Home Back

'Yan sanda sun hana hawan Sallah a Kano

bbc.com 2024/7/6
,

Asalin hoton, FACEBOOK/SANI MAI KATANGA PHOTOGRAPHY

Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Kano ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al'ada a faɗin jihar.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan babbar sallah da za a soma ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami'anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a jihar, kafin sallah da lokacin bukukuwan bayan sallar.

''Haka kuma an haramta duka nau'ikan hawan sallah a lokacin bukukuwan babbar sallah da ke tafe'', in ji sanarwar.

'Yan sandan sun ce sun ɗauki matakin ne sakamakon rahotonnin tsaro da suka samu da kuma tuntuɓar masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, domin tabbatar da zaman lafiyar al'ummar jihar.

Haka kuma 'yan sandan sun shawaraci mazauna jihar da su gudanar da sallar idinsu cikin kwanciyar hankali da lumana, yadda aka saba, ba tare da tashin hankali ba.

''Don haka muna kira ga al'umma da su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusanci'', in ji sanawar.

Hakan na zuwa ne dai bayan da jama'a suka zura ido suna jiran ganin wanda zai yi hawan babbar sallah a jihar, kasancewa akwai ana taƙaddama mai ƙarfi game da sarautar Kano, lamarin da yanzu haka ke gaban ƙuliya.

A ranar 23 ga watan Mayun 2024 ne dai, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da naɗa Muhammadu Sanusi II, a matsayin sarkin Kano na 16, bayan sauke Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma rushe ƙarin masarautun da gwamnatin Ganduje ta yi a shekarar 2019.

People are also reading