Home Back

Kwamitin Mata na Masallacin Salafussaleh dake Ɗorayi ya bai wa Marayu 109, tallafin kayan sawa

dalafmkano.com 2024/5/17

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci masu hali da su ƙara ƙaimi wajen tallafawa Marayu, da abubuwan da suka sawwaƙa domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin taron wa’azantar da Mata kan mahimmancin tallafawa Marayu, tare da kuma tallafawa Marayun da kayayyakin sawa su 109.

Kwamitin Mata na masallacin Salafussaleh da ke unguwar Ɗorayi ƙarama ne ya shirya al’amarin, domin a tallafawa marayun dan suma su samu farin ciki kamar ƴaƴan kowa, wanda ya gudana a cikin malassacin na Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi a ƙaramar hukumar Gwale a Kano.

Da take nata jawabin Malama Baraka Yusuf Hassan, kira ta yi ga al’umma da su ƙara himma wajen tallafawa Marayu da abubuwan a suka sawwaƙa, domin rage musu wani halin ƙuncin rayuwa na yau da kullum.

Yayin taron bada tallafin dai al’umma da dama ne suka samu damar halarta musamman ma Matan yankin da ma na sassan jihar Kano.

People are also reading