Home Back

Ukraine ta bude ofisoshin jakadancinta a nahiyar Afirka

dw.com 2024/5/3

Ukraine ta kaddamar da ofishin jakadancinta na Côte d'Ivoire a ranar Alhamis, kwana guda bayan bude wani da ta yi a Jamhuriyar dimukuradiyyar Congo, a wani mataki na neman yaukaka alaka da kasashen Afirka domin dakile tasirin Rasha a nahiyar.

Karin bayani:Rasha ta bai wa Burkina Faso alkama

Mataimakin ministan harkokin wajen Ukraine Maksym Subkh, ya ce sun bude wani sabon shafin tarihi ta fuskar alaka da Côte d'Ivoire da kuma nahiyar Afirka, bisa umarnin shugaban kasar Volodymyr Zelensky.

Karin bayani:Putin zai gana da shugabannin Afirka

Nan gaba kadan Mr Maksym Subkh zai kai ziyara kasashen Ghana da Mozambique da Bostwana da kuma Rwanda, domin kaddamar da sabbin ofisoshin jakadancin Ukraine a cikin kasashen, bayan na Kinshasa da Abidjan.

Rasha dai ta yi nisa wajen tabbatar da kyakkyawar alaka da kasashen Afirka musamman ta fuskar harkokin da suka shafi tsaro.

People are also reading