Home Back

Sifaniya za ta kara da Jamus a kwata fainal a Euro 2024

bbc.com 6 days ago
Spain

Asalin hoton, Reuters

Sifaniya ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe bayan da ta doke Georgia 4-1 ranar Lahadi a karawar zagaye na biyu.

Georgio ce ta fara cin kwallo a minti na 18 da take leda, bayan da Robin Le Normand ya ci gida.

Daf da za su je hutu ne Sifaniya ta farke ta hannun Rodrigo Hernandez a minti na 39, haka suka je hutu suka kuma koma zagaye na biyu.

Daga nan ne Sifaniya ta kara sa ƙwazo, wadda ta kara na biyu ta hannun Fabian Ruiz, sai Nico Williams ya ci na uku, sannan Dani Olmo ya zura na hudu a raga.

Da wannan sakamakon Sifaniya za ta fafata da Jamus, mai masukin baki a zagayen daf da na kusa da na karshe ranar Juma'a 5 ga watan Yuli.

Ranar Asabar Jamus ta doke Denmark 2-0 a zagaye na biyu, hakan ya sa ta kai kwata fainal a gasar da take karbar bakunci ta Euro 2024.

Sifaniya ba ta ɗauki Georgia da wasa ba a karawar zagaye na biyu a Euro 2024

Luis de la Fuente ya canja ƴan wasa 10 daga cikin wadanda suka ci Albania 1-0 ranar Litinin a wasan cikin rukuni.

Kenan ya fuskanci Georgia da fitattun ƴan wasa da suka hada da matashi, Lamine Yamal da Nico Williams da kuma Pedri.

Aymeric Laporte ne kadai da ba a sauya ba daga ƴan wasa 11 a karawar zagaye na biyu ranar Lahadi, wanda ke murmurewa daga raunin da ya sha jinya.

Ƴan wasan Sifaniya 11: Simon, Carvajal, Le Normand, Morata, Ruiz, Laporte, Rodri, Williams, Yamal, Pedri, Cucurella.

Georgia ce ta doke Portugal 2-0 a wasan cikin rukuni na shida a Euro 2024, haka kuma Georges Mikautadze, ya ci ƙwallo uku.

Sauran da suka ci ƙwallo uku a Euro 2024 sun hada da Ivan Schranz na Slovakia da kuma Jamal Musiala na Jamus.

Ƴan wasan Georgia 1I: Mamardashvili, Kakabadze, Dvali, Kashia, Kochorashvili, Kvaratskhelia, Chakvetadze, Lochoshvili, Gvelesiani, Kiteishvili, Mikautadze.

People are also reading