'Yan Ta’adda Sun Tayar da Bam a Tashar Wutar Lantarkin Najeriya? Minista Ya Magantu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Neja - Wani rahoto da ya yadu a intanet ya nuna cewa abun fashewa ya tashi a tashar samar da wutar lantarkin Zangeru, jihar Niger a ranar Litinin.
Rahoton ya yi ikirarin cewa fashewar bam din ya haddasa raunuka ga wani injiniya dan kasar China, da jami'an tsaro, da ma'aikata da dama, tare da lalata wasu kayan wuta.
Sai dai, a wani martani da ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabu ya yi, ya ce babu wani bam da ya fashe a tashar wutar lantarkin Zungeru, in ji rahoton NAN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar ministan, tashar samar da wutar lantarkin Zungeru tana kan layin tashoshin da ke ba da wuta, kuma tana gudanar da aiki yadda ya kamata.
"Muna da shaidar bidiyo daga Zungeru cewa babu wani abu makamancin haka da ya faru a ranar Litinin kuma duk mai sha'awar tabbatarwa, yana iya zuwa can ya gano."
Jaridar Tribune ta ruwaito rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta musanta rahotannin fashewar bam a tashar wutar lantarkin Zungeru da ke karamar hukumar Wushishi a ranar Litinin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana rahotannin a matsayin “labaran karya” kuma ya ce babu wani abu makamancin haka da ya faru a tashar.
A wani labarin, mun ruwaito cewa adadin mutanen da harin bam na kunar bakin wake ya kashe a jihar Borno ya kai 20, yayin da har yanzu wasu 24 ke kwance a asibiti.
An ruwaito cewa mutane biyu daga cikin wadanda suke jinya sun mutu baya-bayan nan, yayin da aka ce an sallami akalla mutane 16 bayan sun samu sauki.
Asali: Legit.ng