Home Back

'Yan Ta’adda Sun Tayar da Bam a Tashar Wutar Lantarkin Najeriya? Minista Ya Magantu

legit.ng 5 days ago
  • Gwamnatin tarayya ta bakin ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabu ta ce babu wani bam da ya fashe a tashar wutar Zangeru
  • Wani rahoto ne ya bayyana cewa bam ya fashe a tashar wutar kuma har ya haddasa raunuka ga wani injiniya dan China da ma'aikata
  • Sai dai Mista Adebayo ya ce mutane na iya zuwa su gano da kansu, yayin da rundunar 'yan sandan Neja ita ma ta karyata rahoton

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Neja - Wani rahoto da ya yadu a intanet ya nuna cewa abun fashewa ya tashi a tashar samar da wutar lantarkin Zangeru, jihar Niger a ranar Litinin.

Rahoton ya yi ikirarin cewa fashewar bam din ya haddasa raunuka ga wani injiniya dan kasar China, da jami'an tsaro, da ma'aikata da dama, tare da lalata wasu kayan wuta.

Gwamnati ta yi magana kan rahoton tashin bam a Zangeru
Ministan Tinubu ya karyata rahoton tashin bam a tashar lantarkin Zangeru. Hoto: @Jakepor21 Asali: Twitter

Bam ya fashe a tashar Zangeru?

Sai dai, a wani martani da ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabu ya yi, ya ce babu wani bam da ya fashe a tashar wutar lantarkin Zungeru, in ji rahoton NAN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar ministan, tashar samar da wutar lantarkin Zungeru tana kan layin tashoshin da ke ba da wuta, kuma tana gudanar da aiki yadda ya kamata.

"Muna da shaidar bidiyo daga Zungeru cewa babu wani abu makamancin haka da ya faru a ranar Litinin kuma duk mai sha'awar tabbatarwa, yana iya zuwa can ya gano."

Me rundunar 'yan sanda ta ce?

Jaridar Tribune ta ruwaito rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta musanta rahotannin fashewar bam a tashar wutar lantarkin Zungeru da ke karamar hukumar Wushishi a ranar Litinin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana rahotannin a matsayin “labaran karya” kuma ya ce babu wani abu makamancin haka da ya faru a tashar.

Mutanen da bam ya kashe sun kai 20

A wani labarin, mun ruwaito cewa adadin mutanen da harin bam na kunar bakin wake ya kashe a jihar Borno ya kai 20, yayin da har yanzu wasu 24 ke kwance a asibiti.

An ruwaito cewa mutane biyu daga cikin wadanda suke jinya sun mutu baya-bayan nan, yayin da aka ce an sallami akalla mutane 16 bayan sun samu sauki.

Asali: Legit.ng

People are also reading