Home Back

Ko Najeriya ta hau kyakkyawar turba a shekarar farko ta mulkin Tinubu?

bbc.com 2024/7/8
Mai sayar da biredi
Bayanan hoto, Abubakar Sheka, mai sana'ar shayi da biredi ya ce a yanzu mutane da yawa ba sa iya shan shayin.
  • Marubuci, Mansur Abubakar
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kano

A baya 'yan Najeriya musamman matasa sun yi fice wajen hirarrakin da suka shafi ƙwallo a teburan masu shayi.

To sai dai bisa ga dukkan alamu matasan na neman ƙaurace wa wannan ɗabi'a, sakamakon halin matsin rayuwa da aka shiga.

A yayin da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ke cika shekara guda a kan mulkin, Abubakar Sheka, wani mai sana'ar shayi da burodi a jihar Kano, ya ce a yanzu da yawa cikin kwastominsa sun mayar da hankali kan sayen abin da za su iya.

“Musu ko hirar bal, ai ana yin su ne idan ciki ya cika, amma a yanzu yadda ake karɓar kiɗa ai ta abinci kawai ake yi, yanzu duk inda aka taru hirar matsin rayuwa kawai za ka ji,'' in ji matashin mai shayi da biredin.

Ya ce a yanzu mutane ƙalilan ne ke iya sayen biredi, tun bayan da farashinsa ya ninka fiye da sau biyu tun daga watan Mayun bara, sakamakon ƙaruwar farashin fulawa, lamarin da ya sa iyalai da dama suka haƙura daga amfani da burodin, wanda a baya ya zama abinci mafi sauƙi ga iyalai da dama.

Hauwarar farashin kayayyaki da karyewar darajar kuɗin ƙasar, ne manyan abubuwa da aka fi tattaunawa a ƙasar cikin shekara guda da ta wuce.

Duk da cewa Najeriya kamar sauran ƙasashen duniya na fama da matsin tattalin arziki, amma wasu tsare-tsare ko manufofin shugaba Tinubu - da aka rantsar shekarar da ta gabata - ne suka jefa ƙasar cikin wannan hali

A lokacin da ya lashe zaɓe da kashi 37 a bara, shugaba Tinubu ya alƙawarta mayar da ƙasar kan tafarki madaidaici.

Sabon shugaban ya kuma ci karo da matsalolin rashin kuɗi, tare da garkuwa da mutane da cin hanci da rashawa.

Asalin hoton, Reuters

Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Bayanan hoto, A ranar da aka rantsar da shugaba Tinubu ne ya sanar da cire tallafin man fetur.

A lokacin da shugaban ke jawabi jim kaɗan bayan shan rantsuwar kama aiki ne ya yi wata babbar sanarwa.

“Daga yaunzu babu batun tallafin man fetur,” Ya bayyanawa 'yan Najeriya ba atre da bayar da wani wa'adin da matakin zai fara ba, ko wani mataki da zai rage raɗaɗin da za a shiga.

Gomman shekarun da ƙasar ta kwashe tana biyan tallafin man, ya janyo mata kshe maƙudan kuɗi da Tinubu ke ganin zai fi kyau a saka su a wani ɓangre.

“Shugaba Tinubu ya yi jawabin nasa ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe, amma zuwa ƙarfe 11:00 na safen ka fara samun dogayen layuka a gidajen man ƙasar,” in ji Hashim Abubakar wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum..

“Wannan jawabi nasa ne ya janyo farashin man fetur da na sauran kayayyaki suka yi tashin gauron zabo nan take.”

Hauhawar farashin kayyakki ya kai matakin da bai taɓa kai wa ba cikin shekara 18, lamarin da masu sharhi suka alaƙanta da cire tallafin man, hauhwar farshin ya kai kashi 34 cikin 100.

Haka kuma gwamnatin ta fito da wasu manufofi na chanjin kuɗi, inda ta bai wa naira damar samar wa kanta daraja, lamarin da kuma ya janyo sake faɗuwar darajarta. Sai dai nan ma haƙar ba ta cimma ruwa ba, domin naira 10,000 a watan Mayun da ta gabata na daidai da dala 22, amma a yanzu daidai take da dala 6.80.

Wannan ya sa duk wani abu da ƙasar ke sayowa daga waje ya tsada sosai.

Lamarin da ya ƙara jefa mutanen ƙasar cikin ƙarin talauci

Abubakar Ameer wani mai bayar da tallafin abinci ne ga mabuƙata a Kano. Ya kuma ce a shekarar da ta gabata mutanen da ke zuwa neman tallafin abinci sun ninka.

“Dole muka rage ywana abincin da muke bai wa mutane, saboda kowa ya samu abin da zai kai bakin salati,” kamar yadda ya shaida wa BBC.

Gwamnati ta riƙa raba wa mutane tallafin kuɗi da ya kai dala 54 tsawo wata uku ga mutanen da ke cikin tsananin buƙata, amma hakan bai wani rage wahalar ba.

Ministocin Tinubu sun ce suna sane da irin halin matsin rayuwa da ake ciki a ƙasar.

A makon da ya gabata ne ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ya bayar da haƙuri ''kan wahalar da ka shiga saboda tsare-tsaren gwamnati yana mai cewa na lokaci ne, amma sun zama dole ne.''

Ya bayyana matakan da cewa wani ɓangare ne na sake fasalta tattalin arzikin ƙasar, wanda za a jima ana mora idan ya daidata.

“Wannan gwamnati na aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da nufin daidaita tattalin arzikinmu da inganta ci gaban ƙasarmu,” in ji sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, a lokacin da yake gabatar da rahoton ci gaban da gwamnatin ta samu cikin shekara guda.

Asalin hoton, Reuters

'Yan kungiyar kwadago
Bayanan hoto, 'Yan ƙungiyoyin ƙwadago sun yi ta zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar.

Manufar wasu sauye-sauyen shi ne bai wa masu zuba jari daga kasashen ketare karin gwiwa.

An samu karuwar kudade daga masu zuba jari a cikin kusan shekara 10 da suka gabata, to amma a yanzu sun fara raguwa.

"Ina da yakinin nan ba da jimawa kasar za ta samu karin kudi daga masu zuba jari, sakamakon tsare-tsaren gwamnati kan tattalin arziki," in ji Victor Aluyi, babban mataimakin shugaban kamfanin Sankore.

"Ci gaban ba shi da yawa, to amma an samu idan aka kwatanta da yadda abubuwa suke a shekarun baya".

Wani karin kalubale da shugaba Tinubu ya fuskanta a shekararsa ta farko a kan mulki, shi ne matsalar tsaro. An samu mutane da hare-hare a kasar lokacin mulkin shugaban da ya gabace shi.

Yankin arewa maso yammacin kasar ya fuskanci karuwar matsalar garkuwa da mutane. Amma daga watan Maris din shekarar da ta gabata yawan sace-sacen mutanen ya ragu a yankin, kamar yadda rahoton Acled - mai lura da rikice-rikice - ya nuna.

To amma batun sace mutane masu yawa da aka samu a watan Maris ɗin da ya gabata da kuma wanda aka samu cikin maon da ya gabata ya nuna cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da matsalar.

To sai dai gwamnatin na kare kanta

A baya-bayan nan ministan tsaron kasar, Mohammade Badaru ya ce jami'an tsaron kasar sun sama nasarar kashe 'yan bindiga da masu tayar da kayar baya fiye da 9,300, tare da kama kusana 7,000 a cikin shekara guda.

Dangane da batun yakin da rashawa kuwa, shugaban kasar ya samu yabo

"Kawo yanzu, gwamnatin Tinubu ta nuna da gaske take wajen yaki da cin hanci, domin kuwa ta nuna ba sani ba sabo kan duk wanda aka amu da laifin rashawa," in ji Kola Adeyemi, shugaban kungiya mai zaman kanta da ke wayar da kan mutane dangane da rashawa.

Ana kallon matakin da gwamnatin da gwamnatinta ɗauka na dakatar da ministar jin-ƙai - Betta Edu kan zargin karkatar da kuɗin gwamnati - a matsayin abin da ya dace. Ana dai gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa ministar, yayin da ta musanta aikata ba daidai ba.

Wani tsahon babban jami'in hukumar EFCC mai yaki da rashwa a ƙasar, da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa shugaban ƙasar na buƙatar ƙara zage -dantse duk kuwa da alamomin da ya nuna.

“Cin hanci ya shafe gomman shekaru yana ci wa Najeriya tuwo a ƙwarya, don haka bai kamata a auna ƙoarin da ya yi a cikin shekara guda ba, ana buƙatar ƙarin lokaci.''

A duka sauran manufofin, gwamnatin na cewa tana buƙatar ƙarin lokaci wajen cin gajiyar manufofin.

To amma a ganin Mallam Shekar mai sana'ar shayi da biredi, lokaci na ƙara ƙurewa gwamnatin.

“Idan abubuwa ba su inganta ba, musamman fanin tattalin arziki, to dole na lalubo wata sana'ar na haɗa da wannan, ko kuma na jingine sana'ar shayi da biredi na koma wata sana'ar da za ta fisshe ni.”

People are also reading