Home Back

‘Yan ta’adda sun arce da ɗalibai 1,680, sun kashe 180 a hare-hare 70 cikin shekara 10 – UNICEF

premiumtimesng.com 2024/5/17
TASHIN HANKALIN ZAMFARA: ‘Yan bindiga sun sako ɗaliban Maradun 75 bayan kwana 12 da kwashe su

Sama da ɗalibai 1,680 mahara suka arce da su, yayin da kuma suka kashe aƙalla ɗalibai 180 a hare-haren da suka riƙa kai wa makarantu, cikin shekaru 10.

Wannan ƙididdiga dai Hukumar Inganta Karatun Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wato UNICEF ce ta fitar da shi, kakar yadda ƙwararren jami’in UNICEF, Susan Akila ta bayyana, a cikin wata sanarwar da ta fitar, domin tunawa da cika shekara 10 tun bayan sace ɗaliban sakandare ta Chibok da Boko Haram suka yi a Barno.

UNICEF ta nuna damuwar cewa shekaru 10 tun bayan arcewar da aka yi da ɗaliban Chibok su 276, ana ci gaba da kai hare-hare a kan ɗalibai, inda a cikin shekaru 70 aka kai wa makarantu 70 hari.

UNICEF ta ce wannan har yau mahukunta sun ƙi ko sun kasa ɗaukar wani ƙwaƙƙwaran matakin hana afkuwar haka.

“Cikin shekaru 10, rikice-rikicen ta’addanci ya haifar da sace sama da ɗalibai 1,680, waɗanda aka yi wa tattaki har cikin makarantun su aka arce da su; kuma an kashe áƙalla dalibai 180 a hare-haren da aka kai wa ɗaliban har cikin makarantar su.

“Ƙiyasi ya nuna an sace malamai 60, aka kashe 14 a hare-hare fiye da sau 70 a makarantu daban-daban, kamar yadda rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya tabbatar,

“Yawan garkuwa da ɗalibai da ake yi ya na kawo tawaya ga ingancin karatun su.

A cikin 2021, fiye da ɗalibai miliyan 1 suka ji tsoron komawa makaranta bayan hare-haren da aka riƙa kaiwa a makarantu.

Cikin 2020 kuma an rufe kamar makarantu 11,500 sanadiyyar yawaitar hare-hare kan ɗalibai, kamar yadda Nextier ta wallafa a Policy Weekly,” cewar Akila.

UNICEF ta ce yawancin makarantu a Arewa babu kyakkyawan tsarin sanar da gargaɗin tunkarowar barazana a makarantun.

People are also reading