Home Back

RA’AYIN PREMIUM TIMES: Guguwar lodi, jida da jigilar satar kuɗaɗen gwamnati kan idon Gwamnatin Tinubu

premiumtimesng.com 2024/5/4
TSADAR RAYUWA: Jigon APC ya ba Tinubu laƙanin gyara kurakuran da ya tsunduma Ƴan Najeriya cikin tsomomuwa

Duk wani rahoton bin-diddigin yadda kowace ma’aikata, hukuma ko cibiyar gwamnati ta kashe kuɗaɗe da Ofishin Odita Janar na Tarayya ya fitar, cike ya ke da bayanan salwantar maƙudan kuɗaɗen da hatta mahaukaci ba zai iya yin bindiga da su ba, sai dai mai hankalin da ya yi ilmin da bai yi aiki da ilmin ba, sai ta hanyar ɗirka sata kawai.

Gagarimar satar da ake danƙarawa a ma’aikatu ya kai ga har wasu na tababa shin anya akwai shugaba kuwa a ƙasar nan ko babu.

Gagarimar satar rashin kunya ta baya-bayan nan ita ce wadda Odita Janar na Tarayya, ya bada rahoton yadda aka yi wasan kura da wasoson maƙudan kuɗaɗe a ma’aikatun gwamnatin tarayya guda 28 da ɓangarorin hukumomin gwamnatin tarayya, inda aka bankaɗo yadda aka cire Naira tiriliyan 13.95 ta ɓarainiyar hanya, ba tare da sanin waɗanda haƙƙin kuɗaɗen ke kula da kuɗaɗen ba.

Wannan gagarimar satar dai a cikin 2020 rahoton ya ce ta faru. Rahoton ya zo daidai lokacin kuɗaɗen kuɗaɗen waje na gwamnatin tarayya da ke a Babban Bankin Najeriya (CBN), sun ragu da dala biliyan 8.

Ita ma wannan gararrumar ta fari ne daidai lokacin da CBN ya kasa yin bayanin yadda aka yi da maƙudan kuɗaɗen da Najeriya ta ƙwato daga ɓarayin da suka kwashe kuɗaɗe suka kimshe ƙasashen waje, tun daga 2015 zuwa yau.

Waɗannan asusun ajiya kuwa sun zama abin buga misalin yadda hukumomin yaƙi da cin rashawa ba su da ƙarfin tura jaki ruwa, ko ƙarfin halin daƙile satar kuɗaɗe.

Duk da cewa ba a zamanin Gwamnatin Bola Tinubu aka yi wannan gagarimar sata ba, amma dai haƙƙin gwamnatin Tinubu ne ya kawar da wannan mummunar ɗabi’a ta satar dukiyar gwamnati.

Gadangarƙamar da aka yi a shekarar 2020 ta yi munin da har gwamnati ta kai ta yi kasafi biyu, wato wanda duniya ta sani, sai kuma haramtaccen kasafin kuɗi, wanda ya kai adadin kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta ce ta kashe, sun kai Naira tiriliyan 24.54.

Wannan lamari ya faru daidai lokacin kullen korona, yayin da duniya ta afka cikin tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki. Kuɗaɗen ruwa da ake biyan bankuna sun yi yawan fitar hankali. Ba na maganar biyan uwar kuɗin ba.

Saboda haka ba abin mamaki ba ne a Najeriya da aka ce wai an kashe Naira biliyan 2.67 wajen ciyar da yara ‘yan makaranta a lokacin kullen korona. A lokacin fa kowane yaro na can gidan iyayen sa zaune, saboda an ma rufe makarantu.

Kuma bayan nan, sai da Hukumar ICPC a ƙarƙashin tsohon Shugaban Hukuma, Bolaji Owasanoye, ya ce an gano cewa ba aka kashe Naira biliyan 2.6 wajen ciyar da ‘yan makaranta ba. ICPC ta ce kuɗaɗen karkatar da su aka yi cikin aljifan wasu ‘yan ƙaƙuduba.

Yanzu dai idanun kowa kan Tinubu suke, shin zai ɗauki matakin da ya dace, ko kuwa kauda idanu zai yi daga shaiɗancin da jami’an gwamnatin da ta gabata suka tafka.

Don haka Shirin Yaƙi da Rashawa da Gwamnatin Tinubu ke taƙama da tinƙaho da shi, zai zama tatsuniya idan ana bankaɗo irin wannan badaƙala amma ba a yin wani hoɓɓasan ɗaukar matakan da suka wajaba a ɗauka a bisa doka.

Yanzu haka akwai wata Dala biliyan 17 da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ce ta salwanta a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan, har ma ya yi alƙawarin ƙwato kuɗaɗen. Amma shiru, alƙawarin sa ya zama tatsuniya.

To yanzu kuma dama ce da Ministan Shari’a na yanzu Lateef Fagbemi ya samu na ƙoƙarin ƙwato waɗannan maƙudan kuɗaɗe daloli, waɗanda idan aka same su a yanzu, za su ƙara wa asusun kuɗaɗen wajen Najeriya yawa, daraja da ƙarfin arziki.

EFCC ta fara aiki, bisa la’akari da irin nasarorin da ta fara zayyanawa ta samu. To amma ba ba a yi komai ba tukunna, idan aka yi la’akari a irin ɓarnar da aka tafka da wadda ake tafkawa.

Wasu daga cikin garsaƙa-garsaƙan barayin gwamnati su 13 da ake nemam Naira biliyan 772 a hannun su, su na cikin wannan gwamnatin tsundum.

‘Tunda ga gora ga kura, sai a hau duka mu yi kallo.’

People are also reading