Home Back

Kaduna: Sojoji Sun Yi Ajalin Kasurgumin Ɗan Bindiga, Bangaje da Wasu Hatsabibai 3

legit.ng 2024/6/2
  • Wani kasurgumin ɗan bindiga ya gamu da ajalinsa bayan mummunan artabu da dakarun sojojin suka yi a jihar Kaduna
  • Yayin harin, sojojin sun hallaka 'yan bindiga hudu ciki har da hatsabibin ɗan ta'adda, Dongon Bangaje da wasu miyagu uku
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya tabbatar ga manema labarai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Rundunar sojojin Nigeria ta hallaka 'yan bindiga hudu a wani farmaki a jihar Kaduna.

Dakarun 'Operation Whirl Punch da ke Arewa maso Yamma ta yi nasarar hallaka miyagu ciki har da kasurgumin ɗan bindiga, Dongon Bangaje.

Lamarin ya faru a karamar hukumar Giwa da ke jihar inda aka tafka mummunan fada wanda ya yi sanadin mutuwar 'yan bindigan, cewar Channels TV.

Kwamishinan tsaron cikin gida a jihar, Samuel Aruwan ya tabbatar da farmakin da dakarun suka kai a Tumburku da Sabon Sara.

Aruwan ya ce dakarun sun kai farmakin bayan samun bayanan sirri inda suka hango miyagun suna kokarin sauya wuri zuwa Sabon Sara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani hari makamancin wannan, dakarun sojoji sun farmaki kauyen Basurfe da ke Kudu maso Yammacin Kindandan.

Yayin harin, rundunar sojojin ta hallaka mayaka biyu tare da lalata matsuguninsu da suke ba 'yan uwansu kulawa.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading