Home Back

Ba Kamar Yadda Ake Zato Ba, Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Ya Fadi Yawan Albashinsu

legit.ng 2 days ago
  • Tsohon kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Hon. Yakubu Dogara ya fayyace komai kan kuɗin da mambobin suke samu
  • Dogara ya ce bayyana gaskiya kan yawan kudi da suke samu ya zama dole saboda yadda ake zargin suna samun makudan kuɗi
  • Ya ce lokacin da ya ke shugabancin Majalisar albashinsa N400,000 ne da kuma alawus na N25m kacal ba kamar yadda ake zato ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon kakakin Majalisar Tarayya, Hon. Yakubu Dogara ya fadi yawan alawus da ake ba shi.

Dogara ya ce kwata-kwata albashinsa bai wuce N400,000 ba lokacin da ya shugaban Majalisar.

Dogara ya fadi yawan albashin da ya ke samu lokacin shugabancin Majalisar
Yakubu Dogara ya ce N400,000 ne kadai albashinsa lokacin da ya ke shugabantar Majalisar. Hoto: Hon. Yakubu Dogara. Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon kakakin Majalisar ya kuma bayyana cewa ana ba shi alawus na N25m ne a lokacin, Vanguard ta tattaro.

Ya ce fayyace hakan ya zama dole ganin yadda mutane suke zaton makudan kudi ƴan Majalisar ke samu a banza.

"Lokacin da na ke kakakin Majalisar Tarayya, ana ba ni albashin N400,000 a wata da kuma alawus na N25m."
"Na umarci mai kula da kudi na ya bude wani asusun daban domin zuba kudin alawus saboda na al'umma ne wannan."
"Ya yi mun korafi cewa mutane suna yawan roko sai na ce masa idan kudin suka kare ya ci ba shi, idan wasu sun shigo sai ka maye gurbinsu da shi."

- Yakubu Dogara

Dogara ya shawarci ƴan Najeriya da su bar wakikansu su yi musu aiki madadin yawan tambayansu kudi.

Ya ce duk abin da ake fada kan yawan kudi da suke samu kwata-kwata ba haka ba ne kawai zargi ne maras tushe.

Dogara ya caccaki Nyesom Wike

A baya, kun ji cewa tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Yakubu Dogara ya maidawa Nyesom Wike martani kan rikicin da suke yi.

A wasu maganganu da ya yi a shafinsa na Twitter, Dogara ya yi raddi ga Gwamna Nyesom Wike wanda ya zarge shi da rashin dattaku.

Gwamnan na jihar Ribas ya soki Yakubu Dogara bisa zargin cewa ya gagara cika alkawarin da ya dauka, saboda yana goyon bayan Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

People are also reading