Real Madrid vs Dortmund: Abubuwan Sani Dangane da Wasan Karshe na Kofin Zakarun Turai
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
London, United Kingdom - Za a buga wasan karshe na gasar zakarun Turai (UCL) a ranar Asabar, 1 ga watan Yunin 2024.
Wasan ƙarshen za a buga shi ne a tsakanin Borussia Dortmund ta ƙasar Jamus da Real Madrid ta ƙasar Spain.
Za a buga wasan ƙarshen ne a filin wasa na Wembley da ke birnin Landan na ƙasar Ingila, cewar rahoton Goal.com
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Filin wasa na Wembley ya ƙara tsaurara tsaro saboda wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai a ranar Asabar, 1 ga watan Yunin, da nufin kaucewa sake aukuwar rashin bin doka da oda a lokacin gasar Euro 2020.
Real Madrid da Borussia Dortmund za su fafata domin neman lashe gasar zakarun nahiyar Turai (UCL).
Ana yiwa Real Madrid kallon matsayin waɗanda za su yi nasara a wasan yayin da ake kallon Borussia Dortmund a matsayin wacce za ta iya ba da mamaki.
Za a fara wasan ƙarshe na neman cin gasar kofin zakarun Turai a filin wasa na Wembley da ƙarfe 8:00 na dare agogon Najeriya.
Za a gabatar da wasu shirye-shiye kafin a fara wasan.
Dan ƙasar Slovenia, Slavko Vincic ne zai hura wasan ƙarshen a filin wasa na Wembley.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai UEFA, ta tabbatar da zaɓen Slavko mai shekara 44 a farkon watan Mayu.
A Burtaniya, za a nuna wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai a tashar TNT Sports (Discovery+).
A Amurka, za a nuna shi akan tashoshin CBS da TUDN. Ƴan Najeriya za su iya kallo a tashar SuperSport.
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar kwallon ƙafa ta Real Madrid, Toni Kroos, ya bayyana cewa zai yi ritaya daga buga kwallo bayan kammala gasar Euro 2024 a ƙasar Jamus.
Ɗan wasan wanda ya zo Real Madrid daga ƙungiyar Bayern Munich ya sanar da shirinsa na daina taka leda ne a shafinsa na Instagram.
Asali: Legit.ng