Home Back

El Rufai vs Uba Sani: APC Ta Dauki Sabon Mataki Kan Gwamnan Kaduna

legit.ng 2024/10/6
  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya kauracewa halartar taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC a jihar
  • A wajen taron na manyan jiga-jigan jam'iyyar, an kaɗa ƙuri'ar amincewa da Gwamna Uba Sani wanda dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da El-Rufai
  • Taron kwamitin zartarwar ya samu halartar kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero da sauransu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad el-Rufai, bai halarci taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC na jihar ba.

An dai gudanar da taron kwamitin zartarwar na jam'iyyar APC ne a jihar a ranar Asabar, 6 ga watan Yulin 2024.

APC ta amince da Uba Sani a Kaduna
El-Rufai ya kauracewa haduwa da Uba Sani a Kaduna Hoto: @IU_Wakili, @BashirElRufai Asali: Twitter

APC ta amince da Uba Sani a Kaduna

Kwamitin zartarwar wanda shi ne mafi girma na jam'iyyar APC a Kaduna, ya kaɗa ƙuri'ar amincewa da gwamnan jihar Malam Uba Sani, cewar rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron dai na ƴaƴan jam'iyyar APC ne waɗanda a yanzu suke riƙe da manyan muƙamai ko a baya sun taɓa riƙe manyan muƙamai a gwamnatin jihar Kaduna ko a ƙasa.

Kwamitin ya yabawa shirin da gwamnan yake yi na raya yankunan karkara da kuma shirye-shiryen samarwa mata da matasa abin dogaro da kai, rahoton jaridar Daily Nigerian ya tabbatar.

Daga cikin mahalarta taron akwai kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero.

Sauran sun haɗa da mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a yankin Arewa maso Yamma, Datti Babawo da kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Dahiru Liman.

Dangantaka dai tsakanin El-Rufai da Gwamna Uba Sani ta yi tsami a cikin watanni biyun da suka gabata.

Karanta wasu labaran kan El-Rufai

Kwankwaso ya ziyarci El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya karbi bakuncin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa na Abuja.

Nasir El-Rufai ya karɓi baƙuncin jagoran jam'iyyar NNPP ne kwanaki kaɗan bayan ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Daura.

Asali: Legit.ng

People are also reading