Home Back

Bayan Yanke Hukunci Kan Rigimar Sarautar Kano, Kanawa Sun Tarbi Aminu Ado a Faifan Bidiyo

legit.ng 2024/7/4
  • Ana tsaka da rigimar sarauta, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya samu tarba daga dubban Kanawa
  • Dubban jama'a ne suka tarbe shi yayin da ya ke dawowa daga masallacin Juma'a a yau 14 ga watan Yuni a birnin Kano
  • Wannan na zuwa ne bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yi kan korafin Aminu Ado na tauye masa hakki a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake tsaka da rigimar sarautar Kano, Aminu Ado Bayero ya samu tarba daga dubban Kanawa.

Sarkin Kano na 15 ya samu tarba ne yayin dawowa daga masallacin Juma'a a yau 14 ga watan Yuni a birnin.

An tarbi Sarkin ne a cikin wani faifan bidiyo da Masarautar Kano ta wallafa a shafin X a yau Juma'a 14 ga watan Yuni.

A faifan bidiyon, an gano dubban jama'a suna nuna kauna ga tsohon Sarkin inda suke ihun cewa "sai ka yi".

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da aka yanke hukunci kan korafin da Aminu Ado ya shigar bayan tuge shi a sarautar jihar.

Babbar Kotun Tarayya da ke jihar ta ci tarar gwamnan jihar, Abba Kabir N10m kan take hakkin Aminu Ado.

Kotun ta ce umarnin cafke Ado ya saba ka'ida wanda ya tauye masa ƴancinsa na ɗan Adam a Najeriya.

Daga bisani kotun ta ki amincewa da neman tuge Sanusi II daga kujerarsa kamar yadda Aminu Ado ya bukata.

Karin bayani ka tafe....

Asali: Legit.ng

People are also reading