Home Back

Farashin hadin lafiyayyar dafadukan shinkafa na mutum 5 ya tashi daga N13,106 zuwa N16,955

premiumtimesng.com 2024/5/9
Farashin hadin lafiyayyar dafadukan shinkafa na mutum 5 ya tashi daga N13,106 zuwa N16,955

Wani rahoto ya bayyana cewa, farashin dafa hadaddiyar tukunyar dafadukan shinkafa da mutum 5 za su ci su koshi, yayi tashin gwauron zabi daga N13,106 a watan Oktobar 2023 zuwa N16,955 a watan Maris din 2024.

SB Morgan da ta yi binciken ta ce abin ya tashi zuwa kashi 29.3 cikin 100 ne saboda tsadar kayan hadin shinkafar.

Rahoton ya nuna yadda tsadar hadin hadaddiyar dafa-dukan shinkafa ya tashi bayan an daga naira 13,000 zuwa naira 16,000 a wannan shekara.

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kashi 33.20 a watan Maris daga kashi 31.70 a watan Fabrairu.

Rahoton SBM Intelligence ya ce Najeriya ta fuskanci matsalar karancin abinci tsakanin Oktoba 2023 zuwa Maris 2024.

“A cikin wannan lokaci, farashin yin tukunyar shinkafar jollof ya karu da kashi 29.3 cikin 100, daga N13,106 a watan Oktoba zuwa N16,955 a watan Maris 2024,”

Babban abin da ya jawo karuwar a cewar rahoton, shi ne faduwar darajar Naira.

Wannan, in ji ta, ya yi matukar tasiri ga wadatar abinci, musamman yadda har yanzu kasar ta dogara ne kan shigo da abinci domin iya cike gibin da ake samu na rashin shi a afadin kasar.

People are also reading