Home Back

SATAR NAIRA BILIYAN 1.2: ICPC ta gurfanar da jami’in Hukumar Wutar Lantarkin Yankunan Karkara, kotu ta ce a kamo sauran

premiumtimesng.com 2024/6/26
Mun kwato naira biliyan 26 cikin shekara hudu – Shugaban ICPC
ICPC-HQ

Hukumar Daƙile Cin Hanci Da Rashawa a Ma’aikatan Gwamnati, ICPC, ta gurfanar da jami’in Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Yankunan Karkara (REA), wanda ya sace Naira 298 daga manhajar biyan kuɗaɗen hukumar a cikin 2023.

An gurfanar da Usman Ahmed Kwakwa a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ana yi masa tuhuma huɗu.

Kwakwa dai ya na ɗaya daga cikin jami’an hukumar, waɗanda suka sace Naira biliyan 1.2, kamar yadda PREMIUM TIMES ta bada cikakken laharin a cikin watan Maris.

An gurfanar da Kwakwa a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite, amma an bada belin sa a kan Naira miliyan 50.

Akwai sauran jami’ai uku da ya kamata su bayyana a ranar Alhamis a kotun, waɗanda rashin ganin su ya sa Mai Shari’a bada sammacin a kamo su.

Waɗanda Mai Shari’a ɗin ya ce a kamo sun haɗa da Emmanuel Pada Titus, Umar Musa Ƙaraye da Hentientta Onomen Okojie.

Lauya mai gabatar da ƙara ya shaida wa kotu cewa dukkan waɗanda ba su bayyana kotun ba, an kai masu sammacin bayyana kotun, amma suka ƙi bayyana. An ɗage shari’ar zuwa ranar 13 ga Yuni.

DALLA-DALLA: Yadda Jami’an Hukumar Wutar Lantarkin Yankunan Karkara Suka Bar Yankunan Karkara Cikin Duhu:

Yadda korarren Shugaban Hukumar Bada Wutar Karkara ya buɗe asusun banki 37, suka yi wa kuɗaɗen hukumar ƙarƙaf.

Sabon rahoton rahoton da EFCC ta bankaɗo ya ƙara haske dangane da gadangarƙamar satar maƙudan kuɗaɗen Hukumar Bada Wutar Lantarki a Karkara (REA).

Wannan rahoto na EFCC ya tabbatar da binciken musamman da PREMIUM TIMES ta fara yi, wanda ya fallasa tsoffin jagororin REA ƙarƙashin Manajan Darakta Ahmad Salihijo.

Cikin makon shekaranjiya ne Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shugabannin hukumar, ya maye gurbin su da wasu, bayan PREMIUM TIMES ta fallasa satar Naira biliyan 1.2 a hukumar.

Daga nan EFCC ta tura masu bincike domin binciko zargin da ake yi wa Ahmad Salihijo da wasu manyan jami’an hukumar, wato sata ko karkatar da Naira biliyan 12.7, kuɗaɗen da ya kamata su yi bai wa talakawa wutar lantarki da su a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

PREMIUM TIMES dai ta ci karo da rahoton na EFCC, kuma ta dafe, ba ta bari ya suɓuce ba. Ga shi ma za ta bayyana dalla-dalla.

Bayan dakatar da Ahmad Salihijo a ranar 7 ga Maris, tare da shi da Olaniyi Nefuto, Barka Sajou, Sa’adatu Balgore, an naɗa sabbin shugabanni bisa jagorancin Abba Aliyu, matsayin Manajan Darakta.

Ahmad dai ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa shi bai yi sata ba, bai karkatar da kuɗaɗe ko aikata wata almundahana ba.

Binciken Da EFCC Ta Bankaɗo:

1. EFCC ta tabbatar da ƙorafin zargin cewa Ahmad Salihijo ya na da asusun bankuna har asusu 37, kowane kuma ya na ɗauke da BVN lambar sa.

Alhali kuma a fam ɗin rantsuwar bayyana adadin kadarorin sa da ya yi kafin ya fara aiki, ya rantse cewa asusun ajiyar banki 2 kaɗai ya ke da su.

2. Cikin watan Yuni 2023, an karkatar da Naira miliyan 300, kuma aka waske da Naira biliyan 1.2 tsakanin Maris da Yuni 2023, ta hanyar wasu ma’aikatan hukumar su 8.

3. An gano wani Darakta mai suna Alabo Netufo na da kamfani na kan sa, wanda aka riƙa biyan wasu ‘yan kwangila kuɗaɗe ta ƙarƙashin kamfanin.

Sai dai kuma yayin da masu bincike suka ƙara yin ninƙaya, sun ƙara lalubo sabbin harƙallar satar maƙudan kuɗaɗen fitar hankali a Hukumar REA.

Yadda Shugabannin REA Suka Bar Yankunan Karkara Cikin Duhu, Bayan Sun Cika Aljifan Su Da Kuɗaɗen Aikin Samar Da Wutar Karkara:

1. Sun yi cakarkaca da Naira biliyan 12.4, kuɗin korona (COVID-19), wanda gwamnatin tarayya ta ba su. An raba kuɗin an ba su sau biyu. An ba su Naira biliyan 6.2 cikin 2020, sai kuma Naira biliyan 6.2 cikin 2021.

2. An kuma gano yadda su Samihijo ke tirsasa ‘yan kwangila su na ba su kashi 5 bisa 100 na adadin kuɗin kwangilar da aka biya su. Kuɗaɗen kuma an ce a hannu, wuri na gugar wuri suke jibge masu su.

3. An gano wata Naira miliyan 729 da aka biya wasu ‘yan kwangila cikin 2023, da sunan kuɗin ayyukan tuntuɓa, duk dodorido ne, sace kuɗaɗen aka yi.

4. An bankaɗo asusun bankunan Salihijo guda 37, kowane ɗauke da BVN lambar sa.

5. An gano a asusun bankunan akwai bambancin ranakun haihuwar da Ahmad Salihijo ya rubuta wa kan sa.

6. Daga cikin asusu 37, an gano 14 asusun kamfanonincsa ne, 21 na sunan sa ne, sai kuma biyu na wata Bilkisu Salihijo.

7. Lokacin da Salihijo ya cika fam na Hukumar CCB, asusun banki 2 ya mallaka, kuma bai rubuta ya na da kamfani ko ɗaya ba.

8. Kenan an gano ya ƙirƙiro asusun ajiyar kuɗi 27 da kuma wasu biyu. Kuma ya na da kamfanonin da ya ƙirƙira guda 5, wasu 4 kuma ya na da jari ne a cikin su.

9. Wasu asusun ajiyar wasu kamfanonin da aka karkatar da kuɗaɗen, na Access Bank ne, masu lamba: 0094494027 da 0107644861.

10. An dakatar da dukkan ma’aikatan sashen kula da kuɗaɗen hukumar. Kuma EFCC ta bada bayanin yadda aka riƙa karkatar da kuɗaɗen, tare da bayyana sunayen waɗanda suka riƙa karkatar da kuɗaɗen dalla-dalla.

Dabdala Da Naira Biliyan 12.4 Kuɗaɗen Tallafin Cutar Korona:

Cikin 2020 da 2021 an bai wa Hukumar REA Naira biliyan 12.4, domin gagarimin aikin samar da wuta yankunan karkara.

Hukumar ta yi tunanin samar da haske wutar lantarki a wasu yankuna ta hanyar hasken sola a wasu cibiyoyin kula da lafiya na yankunan karkara a faɗin ƙasar nan.

EFCC ta gano cewa a mafi yawan kwangilolin REA ba ta bi umarni da ƙa’idar tantance kamfanonin kwangila da Hukumar BPP ta gindiya wa REA ɗin ba.

EFCC ta gano yawancin kwangilolin duk makusantan shugabannin REA aka ba suka yi, ba tare gayyatar wasu ‘yan kwangila ba.

REA ta bayar da kwangiloli 77 ga ‘yan kwangila, sai aikin tuntuɓa 7 ga wasu ‘yan kwangilar daban-daban.

EFCC ta gano wata Naira miliyan 583,671,227.67 wadda aka rubuta cewa kwangilar Covid-19 ce, amma bayanan da ke cikin na’urar bayyana adadin biyan kuɗaɗen ta Remita, ba ta nuna kuɗaɗen ba. Lamarin da ke nuni da cewa kawai cusa alƙaluman kuɗaɗen aka yi a cikin bayanan kwangila, amma kawai kwashe su aka yi, ba a yi aikin komai da su ba.

EFCC ta gano yadda aka riƙa tura wa ma’aikatan REA Naira miliyan 80, ana fakewa da “aikin bincike da tattara bayanai”, amma duk bagaraswa ce, karkatar da kuɗaɗen aka yi.

EFCC ta gano an riƙa biyan wasu kuɗaɗen kwangilar ba tare da ko takardar rasiɗin tsire ko ta balangu ba.

EFCC ta gano akwai wasu ayyukan Naira biliyan 2 da REA ba ta yi ba a wurare daban-daban na yankunan karkara a faɗin ƙasar nan. Amma kuma REA ta biya kuɗaɗen ga ‘yan kwangila, kamar yadda bincike ya tabbatar.

Yadda Wasu Ma’aikatan REA Suka Fara Amayar Da Kuɗaɗen Da Suka Sace:

An fara ƙwato wasu Naira miliyan 30, kuma jami’ai 4 sun rubuta ranar da za su amayar da Naira miliyan 201.

An karɓo Naira miliyan 207 da wani gida a unguwar Karsana, Abuja sai gidan mai a Kaduna Road, Abuja, yayin da ICPC ta ƙwato Naira miliyan 38.9. Sai filaye uku a Kaduna, sai fulotai uku a Lafiya, Jihar Nasarawa, Mararaba.

An kuma karɓo gidaje na Naira miliyan 46.5 daga hannun wasu mutum 16.

EFCC ta gano cewa daga cikin Naira biliyan 12.4 na Covid-19, aƙalla dai an karkatar da Naira biliyan 6 da ba a yi aikin komai da su ba.

People are also reading