Home Back

Kotu taƙi karɓar roƙon gwamnatin Kano akan shari’ar Masarautu

dalafmkano.com 2024/7/3

Babbar kotun tarayya mai zaman ta a Gyadi-gyadi karkashin mai Shari’a Abdullahi Liman, ta ayyana cewar baza ta dakata daga shari’ar da take yi tsakanin Aminu Babba Dan agundi da gwamnatin Kano ba.

Tun da fari kotun ta yi kwarya-kwaryar hukunci akan batun hurumi inda ta ayyana cewar tana da hurumin sauraron shari’ar kan batun take hakki, hakan ya sanya gwamnatin Kano ta daukaka karar kuma lauyan gwamnatin Barrista Ibrahim Isah Wangida, ya gabatar da roko a gaban kotun inda ya roki kotun da ta dakata tun da dai sun daukaka kara akan matsayar kotun.

Yayin da yake bayyana matsayar sa mai Shari’a Liman, ya ayyana cewar ba zai dakata ba, zai ci gaba da yin shari’ar tun da ba kotun daukaka kara ce ta dakatar da shi ba, kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito.

Idan ba’a manta ba Aminu Babba Dan agundi ya shigar da karar ne yana karar gwamnatin Kano da majalisar dokokin jahar akan batun dokar masarautar jahar Kano ta 2019, wadda majalisar dokokin ta rushe.

People are also reading