Rikicin Siyasa: Gwamna da Magoya Bayansa Sun Dawo Daga Rakiyar Jam’iyyar PDP
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Port-Hacourt, Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya bayyana rashin jin dadinsa kan Jam'iyyar PDP.
Gwamna Fubara ya ce PDP ta gaza wajen cimma muradunsa da na magoya bayansa a jihar Rivers, wanda ya sa kowa ya ke dawowa daga rakiyarta.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa gwamnan jihar na Rivers ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ganawa da kwamitin majalisar dattawa kan kasuwanci a garin Port-Hacourt.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fubara dai ya zama gwamnan Rivers ne karkashin PDP, amma ya ce ba zai yi biyayya ga tsare-tsaren jam'iyyar ba saboda sun kunyata jama'a da yawa.
Gwamnan ya ce shi da magoya bayan shi yanzu sun koma tafiya ne a matsayin kungiya da ke rajin kare dimokuraɗiyya ba wai a matsayin jam'iyyar siyasa ba, inji rahoton Daily Trust.
Har ila yau, Gwamna Fubara ya mahanru kan wani rikici da ya mamaye jihar biyo bayan yunkurin dasa bam da aka yi a wani otel da ke Port-Hacourt a ranar Talata, 25 ga Yuni.
Vanguard ta ruwaito cewa wasu bata gari ne suka yi yunkurin tayar da bam a otel din wanda manyan mutane ke sauka ciki har da mambobin majalisar dattawa.
An ruwaito cewa yan sanda sun samu nasarar kama wanda ake zargi. Gwamna Fubara ya ce wannan yunkurin ya alamta muhimmancin aiwatar da dokar ta ɓaci a jihar Rivers.
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam'iyyar APC ta ce gwamnan jihar Rivers ya kaddamar da wasu ayyuka da Nysome Wike ya yi a matsayin nasa.
APC ta ce ayyukan da Fubara ya kaddamar a lokacin bikin cikarsa shekara daya ba nasa ba ne don haka bai kamata ya rika tutiya da aikin da tsohon gwamnan jihar ya yi ba.
Asali: Legit.ng