Home Back

Yadda Aka Yi Wa Finidi George Kora Da Hali Daga Aikin Kocin Super Eagles

leadership.ng 2024/7/7
Yadda Aka Yi Wa Finidi George Kora Da Hali Daga Aikin Kocin Super Eagles

Kawo yanzu masu sharhi kan al’amuran da suka shafi kwallon kafa na ci gaba da fashin baki a kan sabon kocin babbar kungiyar kwallon kafar Nijeriya ta Super Eagle, mai murabus, Finidi George tun daga lokacin da aka fahimci ba zai iya koyar da ‘yan wasan Super Eagles ba inda tuni hukumar kula da kwallon kafa ta kasa ta dauki umarnin da ministan wasanni ya bayar na cewa a nemo sabon mai koyarwa daga kasar waje wanda zai ci gaba da koyar da tawagar ta Nijeriya.

Wannan shi ne yake nuna cewa tun farko dama ba a yi bincike yadda ya kamata ba wajen daukar Finidi George a matsayin sabon kociyan tawagar Super Eagles kuma ya zama dole a koma baya domin gyara kuskuren da aka tafka.

A cikin Aprilu ne hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta sanar da nada Finidi George a matsayin sabon kocin babbar kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles, matakin da ya ba wa mutane da dama mamaki.

Finidi George wanda tsohon dan wasan Super Eagles ne, ya shafe wata 20 a matsayin Mataimakin tsohon kocin kungiyar, José Peseiro, wanda ya jagorance ta suka lashe lambar azurfa a gasar Nahiyar Afirka (AFCON 2023) a kasar Ibory Coast.

Jim kadan da kammala gasar AFCON 2023 Peseiro dan kasar Portugal ya yi murabus domin kashin kansa, daga nan Finidi George ya ci gaba da horar da ’yan wasan a matsayin riko har zuwa lokacin nada sabon koci.

Bayan ya yi ritaya, ya koma makarantar koyon zama koci, inda a shekarar 2021 ya fara da horar da kungiyar Enyimba FC da ke Jihar Abiya, inda yake aiki har aka gai daukarsa a matsayin Mataimakin Pesero.

Da farko an yi tsammanin wannan matsayin da Finidi ya samu zai taimaka wajen kara daga darajar Gasar Firimiya ta Nijeriya, kasancewar daga gasar ya zama kocin kasar nan sannan kuma idan ya samu nasara kamar ragowar masu koyarwa ne a Nijeriya suka samu saboda zai sa a samu tabbacin cewa nan gaba idan aka sake ba wa wani dama zai yi abin a zo a gani.

Ba a yi tsammanin Finidi George zai zama kocin kungiyar ba, kasancewar an fi sa ran tsohon dan wasan Nijeriya, Emmanuel Amuneke, wanda ake ganin ya fi Finidi kwarewa da sanin makamar aiki, sannan akwai wasu Turawa da ake ganin sun nuna sha’awar horar da kungiyar.

A wata biyu da suka gabata George ya jagoranci Super Eagles a wasannin sada zumunta biyu a kasar Maroko, inda a wasan farko ta lallasa Ghana da ci 2-1, wanda ya kawo karshe shekara 18 a jere da Ghana ke doke ta.

Sai dai Super Eagles ta sha kashi da ci 2-0 a hannun kasar Mali.

Sai dai babban abin da ya saka shakku a zukatan ‘yan kasa shi ne yadda Nijeriya ta kasa samun nasara a wasanni biyu da suka buga a cikin wannan watan a wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya.

Wasan da Nijeriya ta buga 1-1 ta tawagar Bafana-Bafana ta Afirka ta Kudu da kuma wasan da Super Eagles din tasha kashi a hannun kasar

Jamhuriyar Benin da ci 2-1, wanda hakan ya sake jefa tawagar cikin rudani da zullumin cewa shin kasar nan za ta iya kai wa ga matakin neman tikitin zuwa gasar cin kofin duniya?

Finidi Bai Samun Soyayyar ‘Yan Kasa Ba?

Dama dai da yawa daga cikin ‘yan kasa sun nuna shakkunsu a kan kwarewarsa da kuma cancantarsa na zama kociyan tawagar, kuma tuni wasu suka fara kiran cewa ko dai a kore shi ko kuma ya sauka daga kan kujerarsa.

Sannan da yawa daga cikin masoya kwallon kafa a Nijeriya da masu sharhi a kan kwallon kafa sun bayyana ra’ayoyi daban-daban a kan nada Finidi George a matsayin sabon kociyan tawagar Super Eagles ta Nijeriya.

Masana dai sun nuna shakkunsu a kan rashin kwarewarsa wajen koyarwa tare da girman aikin da yake gabansa na koyar da tawaga irin ta Super Eagles wadda a koyaushe ake da burin tawagar ta taka rawar gani a duk gasar da za ta buga ta Nahiyar Afirka ko kuma ta duniya baki daya.

Kafin a bashi ragamar koyar da Super Eagles, kusan sau biyu Finidi George yana neman a bashi dama ya zama kociyan tawagar matasa ta Nijeriya amma duk da haka bai samu nasara ba saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba tun a wancan lokacin.

Amma tun a wancan lokacin, Finidi George ya ce zai ci gaba da zawarcin aikin horar da matasan kasar nan duk da kin daukarsa karo biyu da aka yi, sai dai daga baya ya samu aikin koyar da tawagar Super Eagles gaba daya.

Ya fara zawarcin aikin kocin matasan Nijeriya ‘yan kasa da shekara 17 a shekarar 2018, bayan da Manu Garba ya yi ritaya, a kuma shekarar bara ya sake neman aikin bai samu ba.

Amma daga baya kuma Finidi, mai shekara 49 a duniya ya yi ritaya daga buga kwallo a shekarar 2004 bayan shekara 15 yana sana’ar kwallo, inda ya ci kofin Nahiyar Afirka a 1994 da kofin Lig uku da kofin Turai a shekarar 1995 da Ajad.

Dama ba shi da kwarewar koyar da babbar tawaga

Wannan shi ne matakin da masana suke kai, na cewa bashi da kwarewa kuma bai cancanta ya karbi ragamar koyar da babbar tawaga ba saboda bai taba koyar da wata kasa ba ko babbar kungiya a baya.

Yin ritayarsa ke da wuya ya mallaki lasisin horar da kwallon kafa daga Turai, amma kafin nan ya yi aiki a matsayin darakta a tsohuwar kungiyarsa ta Real Betis da kuma wata karamar kungiya da ya ja ragama a Real Mallorca a shekarar 2013.

Amma dai duk wannan yunkurin da ya dinga yi bai san a gaba zai zama kociyan tawagar Super Eagles ba, abin da bai taba kawowa ba a nan kusa duba da irin yadda aka hana shi aikin koyar da matasa a baya.

Finidi George na cikin ’yan wasan Nijeriya da suka lashe Gasar AFCON 1994 a kasar Tunisiya, kuma su ne suka zama na biyu wajen kayatar da masu kallo a gasar Kofin Duniya a 1994 a kasar Amurka, wanda shi ne karon farko da Nijeriya ta buga gasar.

‘Yan wasan Super Eagles sun yi masa?

Wasu dama suna ganin ba zai iya koyar da tawagar ba, kuma an yi zargin cewa manyan ‘yan wasan da suke cikin tawagar ne suka yi masa girma har ya kasa sarrafa su yadda ya kamata ba kamar matasan ‘yan wasa ba.

Nijeriya tana daya daga cikin kasashen da suke da zakakurai kuma manyan ‘yan wasan da a daidai wannan lokacin tauraruwarsu take haskawa a fadin duniya inda suka buga abin a zo a gani a kakar wasan da aka kammala a Nahiyar turai.

‘Yan wasa irin su Bictor Boniface na kungiyar kwallon kafa ta Bayer Liberkusen da ta lashe gasar Bundes Liga ba tare da ta yi rashin nasara ba da dan wasa Ademola Lookman da ya jagoranci kungiyarsa ta Atlanta ta lashe gasar cin kofin Europa League kuma ya zura kwallaye uku a wasan karshen sun isa misali.

Sannan akwai ‘yan wasa irin su Bictor Osimhen da Sadik Umar da Ndidi da sauran ‘yan wasan da suke ci gaba da haskawa a Nahiyar Turai sun isa a ce Nijeriya tana samun nasarori a dukkan wasanninta da take bugawa.

Sai dai duk da haka akwai bukatar a bashi dama kamar yadda wasu suke fada domin ganin cewa ya saita tawagar, sannan ya kamo bakin zaren kamar yadda ake ganin cewa yayi wuri a ce za a kore shi ko kuma a ce ya ajiye aikinsa.

Yanzu wanne matsayi zai koma?

Bayan da NFF ta amince da kawo dan kasar waje domin jan ragamar Super Eagles, Finidi George zai koma matsayinsa na baya na mataimakin mai koyarwa, wanda a baya ya shafe kusan shekaru biyu a wannan matsayi kafin a nada shi a matsayin mai koyarwa.

Wannan mataki da NFF ta dauka mayar da shi matsayin mataimakin mai horarwa Finidi yake ganin hakan wata kora da hali ne wanda ake cewa ya fi kora da kara ciwo, inda shi kuma ya yanke shawarar yin murabus. A halin yanzu dai rahotanni sun yi da cewa tsahon mai koyar da Super Eagles din Finidi George ya ajiye aiki.

Sai dai abin jira yanzu shi ne wanda zai amince ya karbi aikin duba da halin da tawagar take ciki na rashin tabbas din samun tikitin zuwa gasar cin kofin duniya, a wata mai kamawa ne kuma za a raba jadawalin wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka.

People are also reading