Home Back

"Kungiyar Nadamar Tarayya da Tinubu": Ɗan PDP Ya Yi Shaguɓe ga El-Rufai, Kwankwaso

legit.ng 6 days ago
  • Wani ɗan a mutum Atiku Abubakar ya lissafo waɗanda da kwata-kwata ba su jin dadin yadda ake gudanar da mulkin APC a kasar
  • Abdulaziz Abubakar ya ce wasu mambobin APC suna nadamar tarayya da Tinubu da suka haɗa da Nasir El-Rufai da Yahaya Bello
  • Jigon PDP ya ce El-Rufai ne ya assasa kungiyar sai kuma Sanata Yari babban darakta da kuma Rabiu Kwankwaso babban majibincinta

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar PDP ya yi shagube ga wasu mambobin APC da ba su jin dadin abin da ke faruwa a Najeriya.

Abdul-aziz Abubakar ya lissafo Nasir El-Rufai da Yahaya Bello da Rabiu Kwankwaso wadanda suke kungiyar nadamar tarayya da Bola Tinubu.

Jigon PDP ya yi shaguɓe ga El-Rufai, Kwankwaso da Yahaya Bello
Dan PDP ya fadi wadanda ba su jin dadin gwamnatin Bola Tinubu ciki har da Nasir El-Rufai. Hoto: Nasir El-Rufai, Asiwaju Bola Tinubu, Yahaya Bello. Asali: Facebook

Dan PDP ya fadi mukamin El-Rufai, Kwankwaso

Ɗan PDP wanda ke goyon bayan Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Litinin 24 ga watan Yunin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce El-Rufai shi ne ma'assasin kungiyar yayin Sanata Abdul'aziz Yari ya zama babban darakta sai Kwankwaso babban majibincin kungiyar.

Wannan na zuwa ne bayan rasa mukamin Minista da El-Rufai ya yi da kuma binciken tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

"Sauran wadanda ke cikin kungiyar" - Dan PDP

Sai kuma Kwankwaso wanda ke zargin Tinubu da kitsa duk wata rigima game da dawo da Aminu Ado Bayero a jihar Kano.

Jigon PDP ya lissafo sauran da suka haɗa da Aisha Binani a matsayin shugabar mata sai Yahaya Bello shugaban matasa da kuma Sanata Kabir Marafa mai magana da yawun kungiyar da sauransu.

"Ministocin Tinubu marasa amfani" - Dan PDP

A wani labarin, kun ji kewa wani dan PDP kuma na hannun daman Atiku Abubakar ya shawarci Bola Tinubu ya kori wasu Ministoci.

Abdul aziz Abubakar ya ce daga cikinsu akwai Ministan tsaro, Bello Matawalle da Ministan makamashi, Adebayo Adelabu da sauransu.

Hakan ya biyo bayan yawan korafe-korafen da ake yi kan wasu Ministoci a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu inda aka bukaci ya sallame su.

Asali: Legit.ng

People are also reading