Home Back

Ƙungiyar Ƙwadago Reshen Jihohin Kudu maso Kudu na so a maida Naira 850,000 mafi ƙanƙantar albashi

premiumtimesng.com 2024/4/28
Shekara 8 Tsakanin Buhari da Yan Kwadago: Fallasa ta fi Yabo Yawa, Daga Ahmed Ilallah

Kungiyar Ƙwadago Reshen Jihohin Kudu maso, na so gwamnatin tarayya ta maida mafi ƙanƙantar albashi ya fara daga Naira 850,000.

Shugaban NLC na Jihar Akwa Ibom, Sunny James ne ya bayyana haka a matsayin buƙatar ilahirin ma’aikatan yankin, yayin da ya bayyana a taron jin ra’ayin jama’a, dangane da batun ƙarin albashi, wanda aka yi a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.

James ya nuna rashin jin daɗin cewa wasu jihohin a yankin har yanzu ba su ma fara biyan Naira 30,000 mafi ƙanƙantar albashi, tun bayan yin ƙarin a cikin 2019.

Sai dai kuma James bai bayyana sunayen jihohin da ya ce ba su fara amfani da biyan Naira 30,000 ɗin ba.

Daga nan ya cika da mamakin ganin yadda gwamnonin jihohin Arewa, waɗanda ya ce sun fi sauran jihohi karɓar kaso mai yawa na kuɗaɗen gwamnati fiye da sauran jihohin ƙasar nan, masa kuma a ce su waɗannan gwamnonin ne matsalar ƙin fara amfani da sabon tsarin albashi.

Daga nan shugaban na ƙungiyar ƙwadago ya bada shawarar a riƙa tsigewa tare da kulle gwamnonin da suka ƙi biyan albashin ma’aikatan jihar.

Ya ce Najeriya ta afka cikin tsomomuwa tun daga ranar da aka rantsar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan mulki, yayin da ya cire tallafin fetur.

Sai kuma ya yi kira ga Tinubu ya samar da yanayin da harkokin kasuwanci za su bunƙasa, ta hanyar samar da sahihiyar wutar, kuma a gyara matatun mai tare da gina wasu ƙananan matatun.

Sai dai kuma Shugaban NLC ɓangaren TUC ya haifar da ruɗani da hayaniya, a lokacin da ya ke gabatar da na sa jawabin.

An yi ta yi masa eho da sowa, saboda a cikin jawabin sa, ya ce Naira 447,000 ce ya kamata ta zamo mafi ƙanƙantar albashi, ba Naira 850,000 kamar yadda Shugaban NLC ya bayyana a jawabin sa ba.

 
People are also reading