Home Back

West Ham ta ɗauki Foderingham

bbc.com 2024/7/6

Asalin hoton, West Ham

Wes Foderingham ya lashe kofin Championship na Scotland tare da Rangers a kakar 2015-16
Bayanan hoto, Wes Foderingham ya lashe kofin Championship na Scotland tare da Rangers a kakar 2015-16

Mintuna 2 da suka wuce

West Ham ta ɗauki golan Sheffield United, Wes Foderingham, kan yarjejeniyar shekara biyu.

Foderingham zai koma ƙungiyar ta Hammers a hukumance ranar 1 ga watan Yuli - lokacin da kwantaraginsa zai ƙare a Sheffield.

Ɗan wasan mai shekara 33 ya kama wa Sheffield raga sau 30, ƙungiyar da ta sauka daga gasar Premier League zuwa Championship a bana.

"Na yi sa'ar buga wa ƙungiyoyi masu magoya baya sosai wasa, 'yan kallon da ke matuƙar shauƙin kulob ɗinsu - kuma West Ham ma haka take," in ji Foderingham.

"Abin yana yi min daɗi kasancewata ɗan West Ham!."

Foderingham ya bar Sheffield ne bayan kaka huɗu, amma ya zauna a Rangers, da Swindon, da Crystal Palace, da kuma Fulham.

Shi ne na biyu da West Ham ta ɗauka tun bayan zuwan sabon mai horarwa Jelen Lopetegui bayan ɗaukar ɗan wasan gefe Luis Guilherme.

"Muna farin cikin samun mai tsaron raga da ke da ƙwarewa kamar Wes," a cewar shugaban sashen ƙwallon ƙafa na kulob ɗin Tim Steiden.

People are also reading