Home Back

Crystal Palace ta kara yaga barakar Man United a Premier League

bbc.com 2024/5/19
Erik ten Hag

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta kasa samun gurbin komawa cikin masu fatan buga gasar zakarun Turai a badi, bayan da Crystal Palace ta dura mata 4-0 ranar Litinin.

Kungiyoyin sun kara a gasar mako na 36 a babbar gasar tamaula ta Ingila da suka fafata a Selhurst Park.

Palace ta fara cin kwallo ta hannun Michael Olise daga baya Jean-Philippe Mateta ya kara na biyu saura minti biyar su je hutun rabin lokaci.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Palace ta kara zura biyu a ragar United ta hannun Tyrick Mitchell da kuma Michael Olise, wanda ya ci na biyu a karawar.

Wannan shi ne wasa na uku da suka fuskanci juna, bayan da United ta fara cin 3-0 a League Cup cikin Satumba.

Kwana hudu tsakani Palace ta shiga Old Trafford ta doke United 1-0, inda Joachim Andersen ne ya ci kwallon a minti na 25.

Wannan shi ne karo na biyu da Palace ta zura kwallaye da yawa a ragar United tun bayan 5-0 ranar Asabar 16 ga watan Disambar 1972 tun a gasar rukunin farko.

An zura kwallo 81 a ragar United a dukkan fafatawa a bana, kakar da kwallaye da yawa suka shiga ragarta tun 81 da aka dura mata a 1976/77.

Da wannan sakamakon United tana ta takwas a teburin Premier League da maki 54, iri daya da na Chelsea ta bakwai, wadda ta ci West Ham 5-0 ranar Lahadi.

Ita kuwa Palace ta hada maki uku kenan ya zama 43 tana nan a matakinta na 14 a kasan teburin Premier da tazarar maki daya tsakani da Fulham ta 13.

Sauran wasa biyu ya rage a gaban Palace da za ta je Wolverhampton a karshen mako, sannan ta karbi bakuncin Aston Villa a wasan karshe.

United kuwa wasa uku ne a gabanta, wadda za ta karbi bakuncin Arsenal da kuma Newcastle, sannan ta karkare da zuwa gidan Brighton.

United tana fatan daukar kofi a bana shi ne FA Cup da za ta fafata da Manchester City a wasan karshe.

People are also reading