Home Back

Jihar Kaduna: Rikicin Bashi Da Rashin Sanin Tsarin Gudanar Da Mulki

leadership.ng 2024/4/29
Jihar Kaduna: Rikicin Bashi Da Rashin Sanin Tsarin Gudanar Da Mulki

A Arewacin Nijeriya, akwai Jihar Kaduna; wadda jiha ce mai cike da albarkatu, duk kuwa da cewa; tana fama da matsaloli iri daban-daban da suka hada da yaudara, rashin sanin tsarin gudanar da mulki, rashin gogewa a bangaren sha’anin siyasa da sauran makamantansu. Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan, ko shakka babu; sun fallasa karuwar basussukan da suka yi wa jihar katutu, wanda ya tabbatar da ita a matsayin ta biyu wajen tilin bashi mara ma’ana a Nijeriya.

Wani abu da ya fi daukar hankali shi ne, irin rawar da mazaunin gidan fadar mulki na Sir Kashim Ibrahim ya taka, wanda tun kafin hawansa ya jagoranci amincewa da wani gagarumin lamuni daga Bankin Duniya a lokacin da yake majalisar dokoki. A halin yanzu da ya fuskanci illar rashin kudin da zai gudanar da ayyukansa na raya kasa kuma, sai ya koka da rashin wannan kudi; don gudanar da muhimman ayyukan da ya sanya gaba duk kuwa da cewa, jihar na karbar makudan kudade daga gwamnatin tarayya a kowane wata; domin amfanin daukacin al’ummar wannan jiha ta Kaduna.

Har ila yau, wani al’amari mai daure kai shi ne, rikita-rikitar siyasa da rudani tare da rashin bin ka’ida tattare da wadannan basussuka, wanda shi ne musababin wannan tabarbarewar rashin kudi da ta kai ga sai da sidin goshi ake iya biyan albashi a jihar a halin yanzu.

Basussukan Da Aka Gada

Gwamnan ya bayyana cewa, ya gaji manyan basussuka daga wurin gwamnatin da ta shude; karkashin jagorancin Malam Nasir elrufai, wanda ya kasance a matsayin mai gidansa, na zunzurutun kudi har dala miliyan 587, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 705; idan kowace dala ta tashi a kan Naira 1,200, kamar yadda yake a ranar 3 ga Maris na 2024, sannan da kuma Naira biliyan 85 da kuma Naira biliyan 115 na basussukan ‘yan kwangila.

Tambayoyin da suka dace a wannan gaba su ne:

  1. Shin wannan bashin ya kunshi kudin albashi ne da ba a biya ba ga ma’aikatan wucin gadi, ko kwangila, ko na ‘yan bautar kasa (NYSC), da dai sauran ma’aikata?
  2. Shin wannan bashi ya kunshi kudaden albashin da ba a biya ba ga malamai ko ma’aikatan lafiya ko kuma sauran ma’aikatan gwamnati?

iii. Shin wannan bashi ya kunshi hakkin ‘yan fansho ne da sauran iyalan ma’aikatan da suka rasu?

Alkawari Da Yarjejeniyar Da Gwamna Ya Shiga Da Jama’ar Jihar Kaduna

Wannan yarjejeniya ta 2023, ‘The Sustain Manifesto- 2023’’, ya kunshi ajanda ta 7 tare da mayar da hankali kan ci gaban jihar kamar haka: Samar da tsaro, samar da kayan more rayuwa, samar da manyan cibiyoyi da hukumomi, karfafa ciniki da zuba jari, noma, samar da kwararrun ma’aikata tare da inganta rayuwa al’umma

Wani Hanzari Ba Gudu Ba:

  1. Shin nawa za a kashe wajen aiwatar da wannan ajanda guda 7, sannan kuma a cikin shekaru nawa?
  2. Shin za a aiwatar da ajanda bakwan kuwa, tun da makuden kudaden da ake karba daga gwamnatin tarayya sun samu nakasu?
  3. Yaya batun jin dadin al’ummar Jihar Kaduna?

Rashin amsa wadannan tambayoyi guda uku na nuni da cewa, dimokuradiyyar Nijeriya ko shakka babu gurguwa ce maras armashi.

Filin Kalankuwa Da ‘Yan Kama

A karkashin tsarin bayar da bashi ga kasashe masu raunin tattalin arziki (Debt Sustainability Framework for Low-Income Countries), wanda Bankin Duniya da bankin bayar da lamuni (IMF) ke amfani da shi, karbar bashi ya dogara ne da ikon da kasa da jiha ta ke da shi wajen iya sarrafa bashinta ba tare da bukatar lamuni ba ko rage bashi ko jin kasala wajen biyan bashin ba.

Masana na amfani da abin da ake kira (Debt Sustainability Ratio), wato kwatanta matakan ikon biya tare da yin la’akari da samun kudin shiga da kuma habbakar tattalin arziki da sauran alamu a bangare guda da kuma daya bangaren wato (DSA), wannan wani tsari ne na jarrabawa; wanda ke nuni da iya karbar bashi ko rashin iya karba.

Saboda haka, da zarar matakan sun nuna alama mai kyau, gwamnati a kowane mataki tana iya jin cewa; tana da ikon karbar basussuka, amma kash hakan ba daidai ba ne domin ba a nan gizon ke saka ba.

Amfanin wadannan alamomi shi ne, taimaka wa masu bincike wajen tantance hadarin bashin  da kuma jagorantar yanke shawara, domin kula da bashin a matakai masu dorewa; amma ba don tara bashi saboda kawai gwamnatin mai dorewa ba ce.

Tatsuniya Ko Makircin Siyasa

A cikin wani yanayi mai daure kai, gwamna mai ci a halin yanzu ya samu kansa a karagar mulkin jihar ba tare da wani kwakkwaran tsari na ciyar da jihar gaba ba.

Yayin da lalitar gwamnati ke matukar fuskantar kalubalen rashin kudi, shi kuma wanda ya yi ruwa ya yi tsaki wajen jajibo wa jihar bashin na fuskantar sakamakon wannan aika-aikar da ya yi, su kuma al’ummar jihar suna cikin tsaka mai wuya; domin kuwa ba su san makomarsu ba, musamman a wajen samun romon dimokaradiyya da sauran ayyukan ayyukan ci gaba.

Wani abin kyama kuma shi ne, yadda makircin siyasa irin na Nijeriya ke jawo wa al’umma rashin cigaba, sannan kuma ya fito fili cewa; son kai na masu madafun iko shi ne ya haifar da wannan tabarbarewar tattalin arzikin jihar, kazalika yana fito da matsalar da ke tsakanin mai gida da yaronsa.

Tabarbarewar Tattalin Arziki Da Jin Dadin Jama’a:

Hukumomin da aka damka wa alhakin kula da jin dadin jama’a tare da samar da tagomashi,  tuni sun karkatar da su zuwa hukomin da suka yi kama da aikin kwace. Misali:

I- Hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa da tabbatar da bin doka da oda a jihar, wadda tun farko aka yi wa  matsayin wata hukuma mai sa ido da lura, ta koma sana’ar samar da kudaden shiga ga gwamnati, farautar masu ababen hawa marasa galihu tare da tuhume-tuhumen da su kansu sun karya doka, sannan ga cin  tarar da ake dora wa ‘yan jihar na karin nauyi a kan wanda suke fama da shi.

II- Haka zalika, ofishin yin rajistar filaye sakamakon gazawa da rashin iya aiki, ya haifar da hasashen wani mulki mai kama da tsarin zamba cikin aminci ga masu zuba hannun jari da harka gine-gine.

Bauta Wa Ma’aikatan Gwamnati

Kamar yadda shafin yanar gizo na Hukumar Kididdiga ta Jihar Kaduna (KSBS) ya nuna cewa, adadin mutanen jihar ya kai kimanin miliyan 10.4 a shekarar 2023. Haka kuma, a wata hira da mallam ya yi wajajen Mayun 2016, ma’aikatan jihar dududu ba su kai 100,000 ba.

Sannan, an yi hasashen

 
People are also reading