Gwamnati Da ’Yan Majalisu Na da Laifi a Hauhawar Farashin Kayan Abinci, in Ji Cardoso
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Olayemi Cardoso, gwamnan CBN ya ce sayan kayan abinci da gwamnati da 'yan majalisu suka yi domin rabawa talakawa ya jawo tsadar kayan abinci a kasar.
Cardoso ya bayyana hakan ne a cikin gudunmawar da ya bayar a lokacin taron kwamitin kudi na MPC, wanda aka buga a shafin yanar gizon CBN.
A ranar 25 ga Maris, MPC ta kara yawan ribarta daga kashi 22.75% zuwa kashi 24.75% a wani yunkuri na dakile hauhawar farashin kayayyaki, jaridar The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, a wani rahoton Vanguard hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya a watan Maris ya karu zuwa kashi 33.2%, daga kashi 31.70% a watan Fabrairu.
Hauhawar farashin kayan abinci ya kai kashi 40.01% a cikin wannan watan, wanda ya karu da kashi 15.56% a shekara idan aka kwatanta da kashi 24.45% a watan Maris na 2023.
Da yake tsokaci game da hauhawar farashin kayayyaki, Cardoso ya ce an kasa samun faduwar farashin kayayyaki duk da karin ribar da aka yi a watan Fabrairu.
Channels TV ta ruwaito Cardoso na cewa:
“Duk da cewa an samu daidaiton Naira a kasuwar canji sakamakon matakan da aka dauka a wancan taron na MPC karo na 293, farashin kayayyakin ya ki ya ragu.
“Daga bayanan da aka gabatar wa MPC, akwai alama a bayyane cewa abubuwan da ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki sun ki ba da kai balle bori ya hau har a kawar da su."
Gwamnan na CBN ya ci gaba da cewa akwai bukatar hukumomin kasafin kudi su kara kaimi wajen dakile sababbin abubuwan da ke haifar da hauhawar farashin kayayyakin.
A wani rahoto da Legit Hausa ta fitar a safiyar Juma'a, an ga yadda darajar Dalar Amurka ta kara tashi sama zuwa N1,402 a kasuwar hada-hadar kudi ta duniya.
Wannan na zuwa ne duk da kokarin babban bankin Najeriya (CBN) na ganin Naira ta daidaita domin farfado da tattalin arzikin kasar.
Asali: Legit.ng