Home Back

Amfanin Mangwaro Ga Mata Masu Juna Biyu

leadership.ng 6 days ago
Amfanin Mangwaro Ga Mata Masu Juna Biyu

Kamar yadda aka sani ne, Mangwaro na dauke da sinadarin ‘bitamin da minerals’ masu yawan gaske, wadanda mace mai juna biyu ke bukata a lokacin da take dauke da ciki, domin karfafa jikinta da kuma kula da lafiyar abin da ke cikinta.

Sai dai, ana shawarartar mai juna biyun da kada ta sha wannan mangwaro fiye da guda daya a kowace rana. Sannan, amfanin nasa ga masu juna biyun sun hada da:

– Mangoro na bai wa mata masu dauke da juna biyu kariya daga karancin jini, sakamakon wadataccen sinadarin ‘iron’ da yake da shi, sannan kuma yana kara yawan samar da jinin cikin bargo.

– Haka nan, yana taimaka wa jaririn da ke cikin ciki; ya yi girma cikin koshin lafiya, saboda yana dauke da wadataccen sinadarin ‘folic acid’, wanda ke taimakawa wajen ci gaban girman jaririn da yake cikin cikin uwa.

– Shan mangwaro a cikin watan farkon daukar ciki, abu ne mai matukar muhimmanci da yake taimakawa wajen saurin girman jijiyoyin sadarwa (nerbes).

– Kazalika, yana taimaka wa mata masu ciki; don kawar da matsalolin cushewar ciki, wadanda mata masu juna biyu ke fama da shi sosai, domin kuwa yana dauke da ‘dietary fiber’; wanda ke taimakawa wajen inganta aikin tsarin narkewar abinci.

Tunatarwa:

– Ya kamata mata masu juna biyu su kula, sannan kuma su sani cewa akwai mangwaron da ba na asali ba, ‘yan dabaru aka yi masa don sayar a samu kudi.

– Saboda haka, wajibi ne masu juna biyu su guji amfani da mangwaron da ba na asali ba, ma’ana irin wanda ake sa wa wani sinadari ya yi saurin nuna, domin kuwa ko shakka babu wannan na iya haifar da illa ga lafiyarsu da kuma abin da ke cikin cikinsu.

– Har ila yau, mangwaron yana dauke da wani sinadari mai suna ‘calcium carbide’, wato wani sinadari ne da ake amfani da shi wajen samar da dan itaciya ta hanyar da ba ta dabi’a ba (artificially), wanda hakan na iya karawa mai juna biyu da abin da yake cikin cikinta damar cudanya da sinadarin ‘arsenic da phosphorus’ masu cutarwa.

Haka zalika, akwai illoli masu dimbin yawa da mata masu juna biyu ke fuskanta yayin da suka sha mangwaron da ba na dabi’a bad a suka hada da kamar haka:

– Gudawa

– Chanzawar yanayi

– Ciwon kai

– Jiri ko juwa

– Ciwon ciki

Har wa yau, daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen guje wa amfani da mangwaron da ba na dabi’a ba shi ne, ta hanyar amfani da mangwaron a lokacin kakarsa, ma’ana lokacin da muka sani na asali; wanda a ciki ake girbin mangwaron, sannan kuma mu kauracewa amfani da mangwaron da ake samar da shi bayan kakarsa ta wuce.

Ya Allah ka sauki duk wata mace mai juna biyu lafiya cikin aminci.

Daga kundin Bashir Suraj Adam

People are also reading