Home Back

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi ƙarin bayani, bayan Tinubu ya yi irin faɗuwar da Atiku ya taɓa yi a cikin 2010

premiumtimesng.com 2024/6/26
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi ƙarin bayani, bayan Tinubu ya yi irin faɗuwar da Atiku ya taɓa yi a cikin 2010

Bayan Shugaba Bola Tinubu ya a faɗi a cikin motar da ya hau domin fara kewayawa da shi a Dandalin Eagle Square, wurin da zai duba faretin sojoji a ranar cikar Dimokraɗiyya Shekaru 25, a Abuja, Fadar Shugaban Ƙasa ta yi ƙarin haske, bayan jama’a da dama sun yi ta tofa albarkacin bakin su.

Tinubu mai shekaru 72, ya zame ya faɗi a cikin buɗaɗɗiyar motar, inda nan da nan jami’an tsaron da ke bayan sa suka cicciɓe shi sama suka tayar da shi, ya miƙe, aka fara zagaye tare da shi ya na duba fareti.

“To ai babu wata matsala, domin Shugaban Ƙasa ya ci gaba da gudanar da bikin.” Inji Dada Olusegun, ɗaya daga cikin hadiman Tinubu, kamar yadda ya rubuta a shafin sa na Tiwita, wato X.

Cikin waɗanda suka taya Tinubu jaje, har da Atiku Abubakar, babban ɗan adawa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa wanda Tinubu ya kayar a zaɓen 2023.

“Ina taya Shugaban Ƙasa jajen wannan faɗuwa da ya yi, a lokacin da zai fara duba fareti yayin ƙoƙarin hawa mota. Ina fatan dai lafiya ƙalau yake.” Cewar Atiku, a shafin sa na X.

Faɗuwar Tinubu Irin Wadda Atiku Ya Yi Ce A 2010:

PREMIUM TIMES Hausa ta tabbatar da cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar shi ma ya taɓa yin faɗuwa makamanciyar wannan, a ƙarshen 2010, lokacin da yake ƙaddamar da aniyar sa ta fitowa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2011.

Lamarin na Atiku ya faru ne a babban ɗakin taro na Otal ɗin Sheraton, yayin da ya miƙe zai ya na tafiya domin tsayawa ya yi wa ɗimbin mahalarta taron jawabi.

Atiku ya faɗi, inda ya gurfana ƙasa kan guyawun sa kafin ya ƙarasa wurin da zai yi jawabi.

Faɗuwar dai ba a maida hankali kan ta ba, domin mafi yawan kafafen watsa labarai ba su watsa ta ba, har sai washegari da jaridar LEADERSHIP ta buga hoton Atikun gurfane kan guyawun sa a ƙasa.

LEADERSHIP ba ta yi dogon bayani a kan hoton ba, amma dai a ƙasan hoton ta rubuta: ‘Bad beginning!’

People are also reading