Home Back

Sarautar Kano: Abin da Sanusi II Ya Fadawa Kungiyar Mata Masu Tafsiri a Fadarsa

legit.ng 2024/7/7
  • Yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar Kano, Kungiyar mata masu tafsiri sun ziyarci fadar Sanusi II
  • Matan karkashin kungiyar da ke masallacin marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud sun kai ziyarar domin nuna goyon baya
  • Daga bisani, Muhammadu Sanusi II ya godewa matan inda ya yaba musu kan ayyukan alheri da suke yi a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kungiyar mata masu tafsiri a jihar Kano ta kai ziyarar caffan ban girma zuwa ga Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Kungiyar da ke masallacin marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud a Dorayi ta kai ziyarar domin nuna goyon bayansu.

Kungiyar mata masu tafsiri sun ziyarci Sanusi II a fadarsa a Kano
Muhammadu Sanusi II ya karbi bakwancin kungiyar mata masu tafsiri a jihar Kano. Hoto: Masarautar Kano. Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wani faifan bidiyo da @SanusiSnippets ta wallafa a shafin X a yau Talata 25 ga watan Yunin 2024, matan sun yi ruwan addu'o'i ga Sarkin.

Yayin ziyarar matan sun bayyana goyon bayansu ga Sanusi II tare da yin addu'a ta musamman ga Sarkin.

Daga bisani, sarkin ya yi godiya ga kungiyar matan bisa kyawawan ayyuka da suke yi na addini.

Sarkin ya hore su da su ci gaba da wannan aikin alheri da suke gudanarwa na ilmantarwa da fadakarwa.

Ya ce abin burgewa ne kasancewarsu mata kuma ita mace makaranta ce ta musamman da yara ke fara samun tarbiya.

Daga karshe ya yi musu addu'ar samun nasara a duka ayyukan da suke yi wanda rahamar Allah ke sauak a kansa.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar jihar bayan tuge Aminu Ado Bayero.

Hakimai sun ziyarci sarki Sanusi ii

A wani labarin, kun ji cewa hakimai da dagatai da ga duka kananan hukumomin jihar Kano 44 sun ziyarci Muhammad Sanusi II a fadarsa.

Hakiman da dagatai sun ziyarci fadar ne da shugabannin riko na kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

Musabbabin ziyarar an yi ne domin nuna goyon baya da kuma yin mubaya'a duk da dambarwa da ake ciki.

Asali: Legit.ng

People are also reading