Home Back

Akwai bukatar Ingila ta kawo karshen kamfar nasarar da ta ke damunta- Kwararru

rfi.fr 2024/4/28

Wani dogon sharhi da kwararru suka yi game da tawagar kwallon kafar Ingila, sun bayyana mai horarwa Gareth Southgate a matsayin kwararre ko kuma jajirtacce wajen rasa damar iya lashe wani kofin gasa, ta yadda ya zama koci wanda dama tafi kufce mishi fiye da kowanne manaja a tarihin Ingila.

Wallafawa ranar: 28/03/2024 - 10:54

Minti 1

'Yan wasan tawagar Ingila.
'Yan wasan tawagar Ingila. POOL/AFP

A cewar kwararrun, akwai bukatar Ingila ta kawo karshen rashin nasarar da ta ke fama da ita, ko kuma kishirwar kofunan gasar tsawon shekaru lura da zubi da kuma zakakuran ‘yan wasan da ta ke da su.

Dai dai lokacin da gasar Euro 2024 ke tunkarowa, masanan sun ce akwai fargabar kada tarihi ya sake maimaita kansa game da tawagar ta Ingila karkashin jagorancin Southgate duk da cewa tawagar ta ginu matukar karkashin jagorancinsa amma rashin iya lashe ko da kofi guda ka iya hanasu shiga tarihi.

A wasannin sada zumunta biyu da Ingila ta karbi bakonci cikin kasa da mako guda anga yadda ta sha kaye hannun Brazil da kuma yi canjaras da Belgium dai dai lokacin da Southgate ke shirin fitar da sunayen tawagar shi ta ‘yan wasa 23 da zasu halarci gasar Euro a Jamus.

Southgate dai na matsayin kocin Ingila mafi kwazo a tarihi bayan Sir Alf Ramsey da ya ciyowa kasar kofin duniya 1966, bayan da Southgate ya karbi tawagar daga Roy Hodgson sakamakon tabarbarewarta da ta kai ga ficewa daga gasar cin kofin duniya ta 2014 tun daga matakin rukuni, anga yadda ya kai tawagar ga gasar cin kofin Duniya a Rasha cikin shekarar 2018.

Southgate ya kuma daga likafar tawagar inda har ta kai wasan gab da na kusa da karshe a gasar karon farko cikin shekaru 28, sai dai duk da kokari da jajircewar da ya ke nunawa har zuwa yanzu tawagar ta gaza lashe wani muhimmin kofi.

 
People are also reading