Home Back

Rikicin Sarauta da Shari’ar Zabe Ba Su Taka Masa Burki ba, An Nada Abba Gwarzon Gwamnoni

legit.ng 2024/10/4
  • An ayyana gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya zama jarumin gwamna na shekarar 2024
  • Abba Kabir ya samu karramawar ne bayan kwamitin tantancewa ya zakulo shi tsakanin gwamnonin Najeriya 36 bisa kokarinsa
  • Gwamnatin Kano ta bayyana yadda ta ji da karramawar tare da tare karin haske kan yadda za ta cigaba da ayyukan cigaba a jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Duk da rikicin siyasa da sarauta da gwamnan jihar Kano yake fama da su, jaridar This Nigeria ta zaɓe shi a matsayin gwarzon shekara.

A yau ne jaridar ta bayyana Mai girma Abba Kabir Yusuf matsayin gwarzon gwamna a tsakanin sauran gwamnonin jihohi 36.

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf ya samu lambar yabo. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne a cikin sakon da daraktan yada labaran gwamnatin jihar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf

Jaridar This Nigeria ta ce an zaɓi Abba a matsayin gwarzon shekara ne bisa yadda ya nuna halin maza wajen kawo cigaba a jihar Kano duk da rikice-rikice da yake fuskanta.

Jaridar ta ce ta naɗa kwamiti domin tantance gwamnonin jihohi 36 amma bayan an kammala auna su a faifai Abba ne ya zama na daya.

Karrama Abba: Martanin gwamnatin jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce karramawar za ta karawa gwamnan ƙarfin gwiwar kawo ayyukan cigaba a jihar.

Kwamishinan yada labaran jihar, Baba Halilu Dantiye ya ce gwamna Abba Kabir zai cigaba da shugabanci da zai zama abin kwatance ga sauran jihohi.

Sauran mutanen da aka karrama

A yayin taron an karrama wasu 'yan siyasa a Najeriya cikinsu akwai ministan Abuja, Nyesom Ezonwo Wike da gwamnan jihar Akwa Ibom.

Jaridar This Nigeria ta shirya taron karramawar ne a wajen murnar cika shekaru 25 kan mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Abba zai inganta ilimi a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware makudan kudi domin yin ayyuka na musamman a ɓangare ilimi.

Rahotanni sun nuna cewa ayyukan za su shafi dukkan kananan hukumomin jihar guda 44 domin inganta ilimin karkara da birnin jihar.

Asali: Legit.ng

People are also reading