Home Back

Ƙabilar da ta haramta wa maza auren fararen mata

bbc.com 3 days ago
...
  • Marubuci, Afolabi Akinlabi
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalis
  • Aiko rahoto daga Legas

Yarabawa ƙabila ce da ba su nuna wariyar launin fata wajen zaɓar wanda za su aura, sai dai kuma zuri'ar Ugbo da ke yankin Kararo Ojire a jihar Ondo kan hana maza auren fararen mata.

Masana da mazauna yankin na ganin cewa zuri'ar Ugbo sun fito ne daga birnin Ile Ife kafin su koma inda suke a yanzu watau karamar hukumar Ilaje da ke Ondo.

Wannan dai ya haifar da tambayar ko me yasa aka haramta wa mazan Ugbo su auri fararen mata?

Domin bin diddigin lamarin, BBC ta ziyarci fadar basaraken Olugbo da ke Ugbo, Sarki Obateru Akinruntan, domin neman karin haske kan wannan batu inda muka zanta da basarake Sunday Oluwagbemileke daga Ile Ife.

Mun yi yunƙurin fahimtar hikima game da wannan al'ada da kuma tarihi da suka haifar da haramcin, da kuma tabbatar da ko har yanzu ana aiwatar da ita a Ugbo a yau.

'Dangantakar Olugbo da Moremi'

Sarki Frederick Obateru Enitiolorunda Akinruntan ya bayyana wa BBC cewa zuri'ar Ugbo wani bangare ne na Yarabawa.

Sarkin ya ba da labarin lokacin da sojojin Ugbo suka addabi Ile Ife, wanda hakan ya sa jaruman garin ke fuskantar ƙalubale wajen kare kansu daga farmaki. A lokacin waɗannan hare-hare ne sojojin Ugbo suka kama wata baiwa mai suna Moremi, kuma saboda kyawunta ta zama matar sarkin Ugbo mai suna Olugbo.

Moremi dai ta kasance farar mace kuma kyakkyawa.

A wancan zamani an sha daukar mata marasa nauyi a matsayin mata masu kyau amma kuma kyawun Moremi da haskenta ya sa ta zama matar sarki.

Sarki Frederick ya bayyana cewa, haramta wa mazan Ugbo auren fararen mata ya samo asali ne daga alakar tarihi tsakanin Sarki Olugbo da baiwa Moremi Ajasoro.

'Moremi ce ta haddasa hana auren fararen mata'

Sarki Akinruntan ya bayyana cewa: “Moremi farar mace ce kuma baiwa da ba ƴar zuri'ar Ugbo ba, kuma saboda kyawunta sarkinmu ya aure ta har ta haifar masa yaro.

“Kafin kakanninmu su bar Ife, wasu sojoji ne a Ugbo suke dibar mana abinci kuma a lokacin sun yi amfani da wani manyan kayan aiki da ake kira Kanako, wanda ya ba su damar yin tafiya mai nisa cikin mintuna 20 ko 30 kacal irin wadda aka saba yi a tsawon wata shida.

A lokacin ne kuma suka dawo da kaya da kuma mutanen da suka yi garkuwa da su.

“Moremi kuma na ɗaya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da ita zuwa Ugbo, inda ta zama matar Sarki Olugbo. Ta zauna a can tsawon shekaru kuma ta haifi farin yaro ga Sarki Olugbo.

'Fararen matan kala biyu ne'

Sarkin Ugbo Obateru Akinruntan ya bayyana cewa al’ummar Ugbo sun bambanta fararen mata zuwa iri biyu.

Akwai bambanci tsakanin farar mace da aka haifa a zuri'ar Ugbo da kuma farar mata da ba ƴar ƙabilar Ugbo ba.

Sarkin ya ce: "Farar mace daga zuri'ar Ugbo daban take da farar mace daga wata zuri'ar."

Ya kuma bayyana cewa farar mace daga Ugbo za ta iya yin aure a cikin kabilar, amma ba a yarda da auren bakuwar farar mace kamar Moremi ba.

"Mu da muka san wannan labarin muna gudun auren mata masu launin fata irin su Moremi."

...

Asalin hoton, ooni

Yayin da yake bayyana wa BBC tarihin rayuwar Moremi Ajasoro, Owo Ayekere ta Ile Ife, Sarki Sunday Oluwagbemileke, ya ce an haifi Moremi Ajasoro a birnin Ife. Ta zauna ne a Ile Yekere, a unguwar Ita Akogun a Okerewe.

Sarki Oluwagbemileke ya ƙara da cewa Moremi ta fito ne daga Ife da Offa. Sunan mahaifinta Kurunba kuma mahaifiyarta mai suna Olunbe ’yar asalin garin Offa ce.

Ya ci gaba da cewa: “Mahaifin Moremi mai suna Kurunba ya kasance yana zuwa farauta a garin Offa da ke jihar Kwara a yanzu.

“Mutanen Offa, saboda karfinsa ya burge su, sun gayyace shi ya dinga farauta a dajinsu, kuma sun kasance suna girmama shi sosai. Da zai koma Ife ne suka ba shi ‘ya mai suna Olunbe, wadda ta zama Moremi Ajasoro”.

Sarki Oluwagbemileke ya lura cewa Moremi, wace aka yi wa lakabi da Omoremi, ana tunawa da ita har yanzu a Ile Ife saboda ƙwazonta. "Ile Ife ba zai iya mantawa da Moremi ba saboda gagarumar gudunmawar da ta bayar."

Wace ce Moremi Ajasoro?

...

Asalin hoton, OONIADIMULAIFE/INSTAGRAM

Labarin Moremi Ajasoro labari yana da sarkakiya kuma ana kallonsa ta fuskoki biyu.

A garin Ile Ife, an ɗauki Moremi a matsayin mace mai ƙwazo kuma jarumar da ta ceto birnin daga hannun abokan gābarsa.

Ana gudanar da bikin girmamawa da karrama ta a rana ta biyu ta sabuwar shekara, wanda aka sani da ranar Moremi.

An kuma gina mutummutumin Moremi a Ile Ife domin nuna jarumtarta da sadaukarwarta.

Akasin haka, an ajiye mutummutuminta a Ugbo domin nuna ta a matsayin maci-amana wato wadda ta ci amanar birnin a wajen abokan gaba.

A garin Ugbo kuma, ana bikin tunawa da Moremi a duk shekara a watan Oktoba, domin tunatar da cewa ta ci amanar garin.

People are also reading