Home Back

JIGAWA: Za a kafa cibiyoyi 590 domin ciyar da mutum miliyan 6 abincin azumi cikin watan Ramadan

premiumtimesng.com 2024/4/29
BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙudiri aniyar raba abincin azumi ta yadda zai isa har wurin mutum miliyan shida su amfana, a ƙarƙashin Shirin Ciwarwa A Watan Ramadan Na 2024.

Da ya ke magana lokacin da ya ƙaddamar da rabon kayan abinci, Gwamna Umar Namadi ya ce gwamnatin jihar na sane da irin halin matsatsin rayuwa da ake ciki a ƙasar nan. A kan haka ne ya ce gwamnatin sa ta bijiro da tsare-tsare daban-daban a ƙarƙashin Shirin Ciyarwa na Watan Ramadan da aka bijiro da su.

Namadi ya ci gaba da cewa maƙasudin fito da wannan shiri na ciyarwa lokacin azumin Ramadan shi ne, domin a taimaki mutane su samu abincin da za su ci a cikin watan Ramadan mai albarka.

“Lamarin gaskiya akwai tausayi a ce dai mutum ya yini da azumi a bakin sa, amma lokacin buɗe-baki ya rasa abincin da zai ci. Don haka mu a matakin Gwamnati mu ka ga cewa haƙƙin mu ne mu samar wa al’ummar mu abin da yake addini ya wajibta su samu a sauƙaƙe a lokacin azumi.” Inji Gwamna Namadi.

A jawabin sa wurin ƙaddamar da shirin kayan abincin a Dandalin Taro na Malam Aminu Kano a Dutse, Kwamishinan Ayyukan Musanman, Auwalu Ɗanladi Sankara, ya bayyana cewa za a raba wa gidaje 150,000 ƙananan buhunan shinkafa 150 masu nauyin 25kg, buhunan masara 150,00, katan-katan na taliya 100,000 ga gidaje 150,000.

“A ƙarƙashin kowane gida ɗaya, mun yi kirdado ko hasashen cewa aƙalla mutum biyar za su ci moriyar kayan abincin, waɗanda adadin su zai kai jimillar mutum 700,000 kenan, a faɗin ƙananan hukumomi 27 na jihar.”

“Mai Girma Gwamna Umar Namadi ya kuma amince a kafa cibiyoyin raba kayan abincin azumin Ramadan har 590 a faɗin jihar cikin ƙananan hukumomi 27.

“Za a kafa cibiyar raba abincin azumi biyu a cikin kowace mazaɓa. Amma za a ƙara cibiyoyi biyar a Masarautu biyar na jihar da wasu birane.

“A kowace cibiya za a riƙa ciyar da mutum 300 a kowace rana, har ƙarshen azumi. Saboda haka muna kyautata sa ran ciyar da mutum sama da miliyan biyar abincin azumi.”

Sankara ya ce su kuma ma’aikatan jihar za a raba masu kaɓakin kayan abincin azumi daban. Haka jami’an tsaro, masarautu da sauran wasu ma’aikatan daban.

 
People are also reading