Home Back

Mutanen da kasa ta binne a Papua New Guinea sun haura 2,000

dw.com 2024/7/3
Hoto: Mohamud Omer/International Organization for Migration/AP/picture alliance

Kasar Papua New Guinea ta sanar da Majalisar Dinkin Duniya cewa mutanen da kasa ta binne sun haura 2,000, biyo bayan zaftarewar kasar da ta haddasa bajewar tsaunin Mugalo, a lardin Enga mai tsaunuka a makon da ya gabata.

Faruwar ibtila'in ta sabbaba rushewar gidaje da lalacewar hanyoyi da gonaki, lamarin da ya jefa al'umma cikin mayuwacin hali, sakamakon kangin rayuwa da suka shiga.

Karin bayani:Sojoji na yin bore a Papua New Guinea

Cikin wani sako da ta aikewa Majalisar Dinkin Duniya, Papua New Guinea ta nemi agajinta da ma sauran kasashen duniya, don ceto ta daga mawuyacin halin da ta samu kanta a ciki,bayan mutuwar mutane 670.

Tuni dai kasar Australia ta alkawarta agazawa kasar, kamar yadda mataimakin firaministan kasar Richard Marles ya sanar.

People are also reading