Sarki Muhammadu Sanusi II ya Fadi Abin da Yake Nema Daga Jama'a Bayan Rasuwarsa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano- Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana yadda ya ke son al'umma su tuna shi bayan ya koma ga mahallici.
Gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ce ta dawo da shi karagarsa bayan tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sauke shi.
A wata hira da ya kebanta da Vanguard News, Sarki na 16 wanda rikicin masarauta ya dabaibaye shi ya ce ya na fatan mutane ba za su zage shi bayan rasuwarsa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce daya daga burin da ke zuciyarsa shi ne samun shaida mai kyau idan ya rasu.
Ya ce;
"Ina son idan mutane sun tuna da ni su ce mutumin kirki ne."
Sarkin ya kara da cewa matukar mutum zai shugabanci al'umma, dayan biyu ne – ko dai a zage shi ko kuwa a yabe shi.
Sanusi II ya ce amma fatan da yake yi shi ne bayan ya bar duniya, mutane su fadi alkhairinsa, tare da yi masa addu'a.
Yanzu dai hankulan jama'a sun rabu a sakamakon maido Khalifan na Tijjaniya.
A wani labarin mun kawo mu ku cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya fadi dalilin da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta tsige rawaninsa sa baya.
Ya ce tsohon gwamna Ganduje na zarginsa a wancan lokaci da kin yi masa biyayya, wanda Sanusi II ke ganin ba kwakkwaran dalili ba ne na tsige sarki.
Asali: Legit.ng