Home Back

Maniyyata Miliyan 1.2 Sun Iso Saudiyya Domin Hajjin Bana – Ma’aikatar Hajji Da Umrah

leadership.ng 2024/7/3
Maniyyata Miliyan 1.2 Sun Iso Saudiyya Domin Hajjin Bana – Ma’aikatar Hajji Da Umrah

Ministan Hajji da Umrah na Ƙasar Saudiyya Tawfiq Al-Rabiah, ya sanar da zuwan maniyyata aƙalla miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu, daga kasashe daban-daban na duniya wanda ya ce dukkan matakan tafiyarsu sun tafi lami lafiya kuma alhazan na cikin koshin lafiya.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a birnin Riyadh, Al-Rabiah ya jaddada kudirin Saudiyya na tabbatar da hidimta wa bakin Allah, tare da bayyana kokarin shugabanni na saukaka isar maniyyata zuwa masallatai biyu masu tsarki da kuma wurare masu tsarki, da tabbatar da gudanar da ayyukansu cikin sauki a kwanciyar hankali da samun kulawa.

Ya kuma jaddada muhimmancin bin ka’idoji da umarni don tabbatar da cikakken hidima ga dukkan mahajjata, inda ya yi nuni da kaddamar da wani gangamin ƙasa da ƙasa don wayar da kan jama’a kan illar saɓa ka’idojin aikin Hajji, da ayyukan damfara wanda ake a ƙasashen duniya.

Kazalika gangamin da ake mai taken “Babu Hajji Ba Tare Da Izini Ba”, wanda ma’aikatar harkokin cikin gida ta Makka ke jagoranta, na da nufin wayar da kan jama’a tare da aiwatar da dokokin da suka tsara aikin Hajji, don tabbatar da dukkan maniyyatan sun kammala ibadarsu cikin kwanciyar hankali da lumana.

Al-Rabiah ya ce, sun dauki matakan zaɓar kamfanoni na musamman wajen karbar baki tare da kwararru don inganta yadda ake gudanar da aikin Hajji.

Ya ƙara da cewa a watannin da suka gabata, sama da ma’aikata da shugabannin kungiyoyin alhazai 120,000 sun samu horo cikin yaruka daban-daban na duniya.

Daga ƙarshe ya ce kasar Saudiyya ta yi amfani da duk wani abu da zai taimaka wajen ganin an samu nasarar aikin Hajji na shekarar 1445 bayan hijira.

People are also reading