Home Back

Tallafin mai: Ka daina yaudarar ‘yan Najeriya, Atiku ya tuhumi Tinubu

legit.ng 2024/6/26
  • Atiku Abubakar ya buƙaci shugaban ƙasa ya fito ya faɗawa ƴan Najeriya gaskiya game da biyan tallafin man fetur a gwamnatinsa
  • Wazirin Adamawa ya yi ikirarin cewa cire tallafi duk maganar baka ce, inda ya ce kuɗin tallafin bana 2024 ka iya kai wa N5.4trn
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya nanata cewa babu wani sake fasalin ƙaa da gwamnatin Bola Tinubu ke yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya daina yaudarar ‘yan Najeriya game da hakikanin matsayar gwamnatinsa kan tallafin man fetur.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Laraba.

Atiku da Bola Tinubu.
Atiku Abubakar ya yi ikirarin har yanzun ana biyan tallafin man fetur a Najeriya Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Atiku ya yi iƙirarin gwmanatin Bola Tinubu na biyan makudan kuɗi a matsayin tallafin fetur ba tare da sanin ƴan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaɓen 2023 ya ce kuɗin da gwamnati ta biya da sunan tallafin mai karkashin mulkin Tinubu ya kai N5.4trn a bana (2024).

"A ranar rantsar da shi 29 ga watan Mayu, 2023, Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur kum tun lokacin gwamnatinsa take nanata cewa tallafin ya tafi.
"Wannan duk magace ta baki, na yi mamaki da naga labarin cewa har yanzun gwamnati tana biyan tallafi ba tare da sanin ƴan Najeriya ba."
"A kalamaina na cikar gwamnatin Tinubu shekara ɗaya, na roƙi shugaban ƙasa ya fito ya faɗi gaskiya kan biyan tallafin mai. Taya ake shigo da fetur kuma a rabawa ƴan kasuwa, a wane farashi?"

Wazirin Adamawa ya ƙara da cewa har yanzun ana ware maƙudan kuɗi da sunan biyan tallafin mai fiye da lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

"A yanzu na san cewa kuɗin da aka kashe a tallafin mai ya kai N5.4trn a 2024, wanda ya zarce N3.6trn da aka ware a 2023, shekarar da Tinubu ya ce tallafin mai ya tafi."
"Biyan tallafi da yin karya a kai ba abin alfahari ba ne. Bai kamata ku yaudari ƴan Najeriya da wannan ba," in ji Atiku.

Gwamnati ta shiga taro da NLC, TUC

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya, ƙungiyoyin kwadago da kamfanoni masu zaman kansu sun sake shiga taro kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata

Rahoto ya nuna cewa wakilan gwamnatin tarayya a taron sun haɗa da ministan kuɗi, ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa da ministan kwaɗago.

Asali: Legit.ng

People are also reading